Tsagaita Wuta tsakanin Iran da Isra'ila na Fuskantar Barazana, Trump Ya Gano Masu Laifi

Tsagaita Wuta tsakanin Iran da Isra'ila na Fuskantar Barazana, Trump Ya Gano Masu Laifi

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce duka ƙasashen Isra'ila da Iran sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma
  • Trump ya ja kunnen Isra'ila da kada ta sake jefa bama-bamai kan Iran, yana mai cewa lokacin yaƙi ya wuce a tsakanin ƙasashen biyu
  • Wannan dai na zuwa ne bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila a daren ranar Litinin, 23 ga watan Yuni, 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

USA - Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya zargi kasashen Isra’ila da Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma bayan kusan mako biyu ana ɓarin wuta.

Shugaba Trump ya ce duka ƙasashen biyu sun karya yarjejeniyar sakamakon musayar wutar da suka yi bayan dokar tsagaita wutar ta fara aiki yau Talata.

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka.
Shugaban Amurka ya zargi Isra'ila da Iran ta karya dokar tsagaita wuta Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Donald Trump ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai gabanin tashinsa zuwa taron ƙoli na ƙasashen NATO da za a gudanar a birnin The Hague, Sky News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yaki zai dawo sabo: Isra'ila ta ce za ta cigaba da kai hari Iran bayan tsagaita wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Trump ya zargi Isra'ila da Iran da take yarjejeniya

Donald Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda kasashen biyu ke ci gaba da harbawa juna makamai masu linzami, inda ya ce:

“Ban ji daɗin irin yadda Isra’ila da Iran ke kokarin take yarjejeniyar ba. Ina matuƙar damuwa da irin yadda Isra’ila ke tafiyar da al’amura.”

Trump ya nuna cewa ya damu matuka da ƙarin hare-haren da Isra'ila ta kai, fiye da na Iran, yana mai cewa hakan na iya haifar da matsala a yankin da tuni ke fama da rikice-rikice.

Shugaban Amurka ya yi ikirarin rusa shirin Iran

A game da batun makaman nukiliyar Iran, Trump ya tabbatar da cewa "shirin samar da makaman nukiliyan Tehran ya rushe gaba ɗaya."

“Iran ba za ta sake gina shirin ta na makaman nukiliya ba. Mun gama da hakan tun tuni,"

- inji Donald Trump.

Shugaban Amurka ya gargaɗi Isra'ila da ta dakatar da hare-haren da ta shirya kai wa kan Iran, yana mai cewa dole ta yi biyayya ga yarjejeniyar tsagaita wuta, cewar rahoton Al-Jazeera.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Iran ta kai hari Isra'ila, 'ta rusa yarjejeniyar tsagaita wuta'

Shugaba Trump ya buƙaci Iran da Isra'ila su kai zuciya nesa.
Shugaban Amurka ya gargaɗi Isra'ila kan ci gaba da kai wa Iran hari Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya ja kunnen Isra'ila

“Idan Isra’ila ta jefa bama-bamai kan Iran yanzu, hakan zai kasance babban laifi na take doka. Yanzu ba lokacin hakan bane.”
“Isra’ila, ku dawo da jiragenku na yaƙi gida, yanzu. Wannan lokacin ba na kai hari bane," in ji shugaban Amurka.

Trump ya ja kunnen Isra’ila cewa kada su ƙara hura wutar rikici ta hanyar kai hari kan Iran, yana mai cewa abubuwan da ke faruwa a yanzu na iya ɓallewa zuwa gagarumar fitina idan ba a daidaita ba.

Isra'ila ta yi barazana sake kai hari Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Isra'ila ta yi barazanar ci gaba da kai hare-hare kan Iran duk da shugaban Amurka ya sanar da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce Iran ta karya yarjejeniyar.da aka cimma ta hanyar harba makamai masu linzami kan ƙasar.

Sai dai gwamnatin Iran ta musanta zargin da Isra’ila ke yi cewa an sake harba makamai zuwa kasarta bayan kiran zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262