Abin da Ya Faru a Qatar bayan Iran Ta Harba Makami Mai Linzami kan Sojojin Amurka
- Gwamnatin Qatar ta ce na'u'rorin kakkaɓo makamai sun yi nasarar daƙile harin da Iran ta yi nufin kai wa sansanin sojin Amurka na Al Udeid
- Ma'aikatar tsaron Qatar ta bayyana cewa babu wanda ya ji rauni ko rasa rai sakamakon harin, wanda Iran ta kai da nufin ramuwar gayya
- Wannan ma zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lamarin da ya ja hankalin duniya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Qatar - Gwamnatin Qatar ta bayyana cewa na'urorin tsaron sama sun yi nasarar daƙile makamin da Iran ta harbo kan sansanin sojin Amurka na Al Udeid da ke ƙasarta.
Ma’aikatar Tsaron Qatar ta sanar da cewa babu wanda ya samu rauni ko ya rasa rai sakamakon harin wanda Iran ta kaddamar da nufin ramuwar gayya kan Amurka.

Source: Twitter
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 23 ga watan Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Qatar ta daƙile harin da Iran ta kai kan sojin Amurka
Ma'aikatar tsaron Qatar ta kara da cewa jajircewar dakarun sojin sama da kuma matakan kariyar da ƙasar ta ɗauka ne suka taimaka wajen daƙile harin.
Har ila yau, ma’aikatar ta ƙara da cewa Qatar da sararin samaniyarta suna cikin tsaro, kuma dakarun tsaron ƙasar sun shirya tsaf domin tunkarar kowanne irin barazana.
Wannan dai na zuwa ne bayan Majalisar Tsaron Iran ta bayyana cewa harin makami mai linzami da ta kai sansanin sojin Amurka na Qatar ba shi da nufin taɓa fararen hula.
“Wannan matakin ba barazana ba ce ga ƙawarmu Qatar ko jama'arta. Jamhuriyar Musulunci ta Iran na nan daram wajen ƙarfafa dangantakar zumunci da ke tsakaninta da Qatar.”
Qatar da nuna ɓacin ranta da matakin Iran
Amma a nata ɓangaren, Qatar ta yi Allah wadai da harin tana mai cewa hakan cin mutunci ne ga ƙasar.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar, Majed al-Ansari, ya bayyana harin da dakarun juyin juya halin Iran IRGC a matsayin wanda ya karya dokar ƙasa da ƙasa.

Source: Getty Images
"Wannan hari ya karya dokar ƙasar Qatar da sararin samanta, haka kuma ya saɓa wa dokar Majalisar Ɗinkin Duniya."
"Mu a Ƙasar Qatar muna da ‘yancin maida martani kan wannan ƙeta dokar da aka yi bisa ga ka’idojin doka ta ƙasa da ƙasa,” in ji al-Ansari a cikin wata sanarwa.
Ya ƙara da cewa jami'an tsaron Qatar sun samu nasarar daƙile harin kuma sun kankaɓo makaman Iran da suka nufi sansanin sojin Amurka a ƙasar.
Kasashe sun shirya taimakon Iran
A wani labarin, kun ji cewa Rasha ta yi ikirarin cewa ƙasashen da dama sun nuna a shirye suke su bai wa Iran makaman nukiliya bayan harin da Amurka ta kai.
Mataimakin shugaban majalisar tsaro na Rasha, Dmitry Medvedev, ya bayyana cewa a halin yanzu, ƙasashen da a baya ba su goyon bayan Iran, sun canza shawara.
Medvedev ya ce duk da hare-haren ba su yi mummunan ɓarna sosai ba, akwai yuwuwar Iran ta ci gaba da shirinta na mallakar malamin nukiliya.
Asali: Legit.ng


