Yaƙin Iran da Isra'ila Ya Kawo Hargitsi a Taron UN, Jakadu 2 Sun Yi Musayar Baƙaƙen Kalamai

Yaƙin Iran da Isra'ila Ya Kawo Hargitsi a Taron UN, Jakadu 2 Sun Yi Musayar Baƙaƙen Kalamai

  • Rigima da ce-ce-ku-kuce ta ɓarke tsakanin jakadun kasashen Iran da Isra'ila a taron Majalisar ɗinkin duniya da aka yi a Amurka
  • Jakadan kasar Iran, Amir-Saeid Iravani ya zargi Isra'ila da keta dokokin ƙasa da ƙasa a rikicin da ke faruwa a tsakaninsu kwanakin nan
  • Sai dai wannan kalamai ba su yi wa jakadan Isra'ila daɗi ba, wanda nan take ya maida masa martani da zafafan kalamai a ɗakin taron

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

New York, USA - Jakadun Iran da Isra’ila sun yi mummunan rikici da juna yayin taron Majalisar Dinkin Duniya na Tsaro da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

A taron, Iran da Isra'ila sun zargi juna da karya dokar ƙasa da ƙasa a hare-haren da suke kai wa juna tun ranar Juma'a ta makon jiya.

Kara karanta wannan

Ana shirin Juma'a, Iran ta sake harba makamai masu haɗari kan Isra'ila, ta yi ɓarna

Amir-Saeid Iravani na Iran da Firaministan Isra'ila.
An yi musayar yawu mai zafi tsakanin Iran da Isra'ila a taron Majalisar Dinkin Duniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jakadan Iran ya tona ɓarnar da Isra'ila ke yi

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir-Saeid Iravani, ya nuna yadda hare-haren Isra’ila suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula a Iran, rahoton Aljazeera.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iravani ya ɗaga hotunan wasu ’yan ƙasarsa watau Iran da suke yara ƙanana da suka mutu sakamakon bama-baman da Isra’ila ta jefa masu.

“Aƙalla mata biyu masu juna biyu da jariransu da ke ciki sun mutu a rana ɗaya da Isra’ila ta kai hari kan gidan talabijin na Iran IRIB a lokacin da ake watsa shirye-shirye kai tsaye,” in ji Iravani.

Iran ta zargi Isra'ila da karya dokar ƙasa da ƙasa

Jakadan na Iran ya bayyana cewa hare-haren Isra’ila suna karya dokokin ƙasa da ƙasa, kuma ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta ɗauki mataki.

Ya ƙara da cewa:

“Idan Majalisar Tsaro ba ta ɗauki mataki ba yanzu, hakan zai nuna cewa dokokin ƙasa da ƙasa ana amfani da su ne bisa son rai.

Kara karanta wannan

Iran ta jefa yahudawa sama da 8,000 cikin mawuyacin hali da ta kai kare hare kan Isra'ila

"Idan tsarin hana yaɗuwar makaman nukiliya ya rushe, to, wannan Majalisar za ta kasance da hannu a cikin abin da ya faru tare da gwamnatin Isra’ila.”

Jakadan Isra’ila ya maida martani a fusace

Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya soki takwaransa na Iran, inda ya zarge shi da "kuka na karya" da kuma ƙoƙarin ɓoye ainihin gaskiya.

“Mista Iravani, kai ba ka da wata damar kiran kanka da wanda aka zalunta. Kai ba ma jakada ba ne, kai kura ce da ke sanye da rigar jakada, kuma mun gaji da yin kamar ba mu san haka ba,” in ji Danon.
Iran da Isra'ila sun zargi juna a taron UN.
An yi musayar yawu a taron Majalisar Dinkin Duniya kan yakin Iran da Isra'ila Hoto: @Netanyahu, Getty Images
Source: Getty Images

Danon ya soki Iran kan harin makami da ta kai a wannan makon wanda ya lalata wani asibiti a garin Beersheba da ke Kudancin Isra’ila.

“Ba mu jin kunyar kare kanmu. Ba mu jin kunyar kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran. Ba mu jin kunyar shawo kan barazanar da ke fuskantar mu,” in ji shi.

Makamai 2 sun faɗa kan yankunan Jordan

A wani rahoton, kun ji cewa ana zargin wasu jirage marasa matuƙa da ake amfani da su a matsayin makami sun faɗa yankin ƙasar Jordan.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun ayyana ranar azumi da addu'oi domin zaman lafiya a Najeriya

Rahoto ya nuna cewa an zaton an harbo makaman ne a yakin da ke faruwa tsakanin ƙasar Iran da kuma Isra'ila.

Jami'an tsaro sun bayyana cewa jirage marasa matuƙa da ake kai hari da su sun faɗo a Jordan kuma sun jikkata wata yarinta da lalata dukiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262