Ana Shirin Juma'a, Iran Ta Sake Harba Makamai Masu Haɗari kan Isra'ila, Ta Yi Ɓarna

Ana Shirin Juma'a, Iran Ta Sake Harba Makamai Masu Haɗari kan Isra'ila, Ta Yi Ɓarna

  • Iran ta sake harba makamai masu linzami zuwa kasar Isra'ila a yau Juma'a, 20 ga watan Yuni, 2025 yayin da rikici ke ƙara ƙamari
  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta Isra'ila watau MDA ta ce akalla mutane biyu sun jikkata a sababbin hare-haren da Iran ta kai
  • Rundunar soji ta yi iƙirarin cewa ta harbo wasu daga cikin jirage marasa matuƙa da Iran ta cillo, amma duk da haka wasu sun sauka a kan gine-gine

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - Ƙasar Iran ta ƙara cilla makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da ke fashewa kamar bam kan biranen Isra'ila.

Duk da rundunar sojin saman Isra'ila ta yi koƙarin kare harin, amma makaman sun fasa wasu wurare tare da jikkata aƙalla mutane biyu.

Iran ta kara kai farmaki Isra'ila.
Mutum 2 sun jikkata da Iran ta sake harba makamai kan Isra'ila Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC News ta tattaro cewa Hukumar agajin gaggawa ta Isra’ila (MDA), ta ce mutane biyu sun jikkata a harin na yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Iran ta ƙara yunƙurowa tun da asubah, ta yi ɓarin wuta kan Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iran ta jikkata Isra'ilawa a sabon hari

Daya daga cikinsu shi ne saurayi dan shekara 16 wanda ke cikin mawuyacin hali sakamakon raunukan da ya samu a jikinsa.

Sai kuma wani namiji wanda ya girma da ya kai kusan shekara 54, wanda ke cikin matsakaicin hali da rauni a ƙasa da jikinsa.

A wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, kuma tashar Al Jazeera ta tabbatar da sahihancinsa, an ga jirginn yakin Isra’ila kirar F-16 na ƙoƙarin harbo makaman Iran.

Bidiyon ya nuna lokacin da jirgin sojin Isra'ila ya harbo jirgi mara matuƙa da Iran ta cillo, inda ya faɗo ƙasa kuma ya fashe.

Wannan lamari ya faru ne a yankin Deraa, kusa da iyakar kudu maso yammacin Siriya.

MDA ta ce an samu karin waɗanda suka jikkata

A wata sanarwa da hukumar agaji ta MDA ta sake fitarwa, ta bayyana cewa tana ba da kulawa ga mutum 17 da suka jikkata, ciki har da mutane uku da ke cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Yaƙin Iran da Isra'ila ya yi gagarumar ɓarna, an kashe mutane sama da 600

Hukumar ceto da ba da agajin gaggawa ta MDA ta tabbatar da cewa mutane biyu sun jikkata a sabon harin makamai da Iran ta kai Isra'ila.

Iran ta ci gaba da kai hare-hare.
Mutane sama da 10 sun jikkata da sabon harin da Iran ta kai ƙasar Isra'ila Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wata sanarwa da hukumar ts fitar, ta ce:

“Likitocin MDA na ci gaba da ba da kulawa ga waɗanda suka jikkata, inda suka dauki saurayi ɗan shekara 16 zuwa asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon raunukan da ya ji a jikinsa.
"Sai kuma wani dattijo mai shekara 54 da ya ji ɗan karamin rauni a jikinsa sakamakon harin. Mun kuma kara samun wasu mutum 14 da suka ji raunuka."

Isra'ila ta kai farmaki asibiti na 3 a Tehran

A wani labarin, kum ji cewa hukumomin ƙasar Iran sun tabbatar da cewa Isra'ila ta jefa bama-bamai kan wani asibiti a birnin Tehran.

Ma'aikatar lafiya ta Iran ta bayyana cewa harin ya lalata motocin ujila, waɗanda ake amfani da su wajen ɗaukar marasa lafiya.

Ta yi kira ga Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar Agaji ta Ƙasa da Ƙasa (ICRC), da su kare asibitoci, ma’aikatan lafiya da kuma marasa lafiya daga hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262