Iran Ta Sake Yin Luguden Wuta kan Isra'ila, Ta Ragargaza Babbar Cibiyar Kimiyya

Iran Ta Sake Yin Luguden Wuta kan Isra'ila, Ta Ragargaza Babbar Cibiyar Kimiyya

  • Isra’ila ta dade tana kai hare-hare kan masana nukiliya na Iran, amma yanzu masana kimiyya na Isra’ila na fuskantar barazana
  • Iran ta harba makami zuwa cibiyar kimiyya ta Weizmann a Isra’ila, inda ya haifar da mummunar barna ga dakunan bincike
  • Duk da babu asarar rayuka, harin ya girgiza Isra’ila, inda Iran ta bayyana cewa martani ne bisa kashe masananta da Isra’ila ta yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Isra'ila - A tsawon shekaru, Isra'ila ta riƙa kai hari kan masana nukiliya na Iran, da fatan za ta hana ci gaban shirin nukiliyar Iran ta wannan hanyar.

Sai dai a cikin 'yan kwanakin nan da yaki ya barke tsakanin kasashen biyu, masana kimiyya a Isra'ila sun tsinci kansu a cikin tashin hankali bayan halin Iran.

Kara karanta wannan

An bayyana ƙasa 1 da za ta iya kare Iran yayin da Amurka ke shirin kai hari Tehran

Iran ta kai mummunan hari kan babbar cibiyar bincike ta Isra'ila, ta lalata Weizmann
Makamai masu linzami da Iran ta harba na ci gaba da sauka a cikin babban birnin Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta farmaki cibiyar kimiyya ta Weizmann

Kafar watsa labarai ta AP News, ta rahoto cewa Iran ta harba wani makami mai linzami zuwa Isra'ila, kuma ya sauka kan babbar cibiyar bincike ta Isra'ila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa, makamin Iran ya yi babbar barna kan cibiyar kimiyya ta Weizmann, wadda aka sani da aikinta a fannin kimiyyar halittu da kimiyyar lissafi, da sauran fannoni.

Kodayake babu wanda ya mutu a harin da aka kai wa Weizmann, amma an ce ya haifar da mummunar barna ga dakunan gwaje-gwaje da dama a harabar cibiyar.

Wannan ya jawo rushewar binciken kimiyya da aka shafe shekaru ana yi kuma ya aika da sako mai ban tsoro ga masana kimiyya na Isra'ila cewa yanzu sune abin hari a rikicin da ke ƙaruwa da Iran.

Iran ta ce ta farmaki babbar cibiyar Isra'ila domin zama martani kan kashe masana kimiyyarta
Iran da Isra'ila na ci gaba da musayar wuta tskaaninsu, inda aka lalata gine-gine masu yawa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin Iran na kai hari kan cibiyar Weizmann

Duk da cewa Isra'ila ta fi yi wa Iran barna a fuskar kimiyya da shirin nukiliya a yakin nan, amma ana ganin harin da aka kai wa Weizmann a wannan makon zai iya canja komai.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta tura jiragen yaki, sun tarwatsa sabuwar cibiyar hada nukiliya a Iran

Kodayake cibiyar bincike ce mai fannoni da yawa, Weizmann, kamar sauran jami'o'in Isra'ila, tana da alaƙa da cibiyar tsaro ta Isra'ila, gami da haɗin gwiwa da manyan masana'antu kamar Elbit System.

Iran ta ce ta kai harin ne saboda cibiyar tana wakiltar "kimiyyar Isra'ila ne", kuma harin ya zama martani na: "Kun kashe masananmu, don haka mu ma za mu rama kan manyan masananku."

An lalata ginin cibiyar da dakunan gwaje-gwaje

Rahoton Economic Times ya nuna cewa an kai hari kan gine-gine biyu a harin, ciki har da ɗaya mai ɗauke da dakunan gwaje-gwaje na kimiyyar halittu da kuma wani sabo da ake ginawa don nazarin kimiyyar sinadarai.

An rufe harabar cibiyar tun bayan harin, yayin da aka ce an ga manyan tarin duwatsu, ƙarafuna da sauran tarkace sun warwatse a harabar cibiyar.

Yakin Iran da Israila ya shafi Jordan

Rahoto ya zo cewa rikicin Iran da Isra'ila na ƙara kamari har ana zargin wasu makamai 2 sun kauce hanya, sun faɗa yankuna a ƙasar Jordan.

Hukumomin Jordan sun tabbatar da lamarin, sun faɗi ɓarnar da makaman suka yi. Yanzu dai an rasa dukiya kuma an samu wanda ta ji rauni.

Ana zargin cewa gwamnatin Jordan ba ta ba kasar Iran hadin-kai a yakin da ake yi, ta na taimakawa wajen hana a taba Israila a rikicin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com