Iran Ta Ƙara Harba Makamai Masu Haɗari Guda 30 kan Isra'ila, An Ji Abin da Ya Faru
- Ƙasar Iran ta ƙara harba makamai masu linzami guda 30 kan Isra'ila a daren ranar Laraba yayin da yaki ke ƙara ta'azzara
- Rundunar sojojin Isra'ila ta tabbatar da kai hare-haren amma ta ce an yi nasarar tare su ba tare da sun sauka ba ballantana su yi ɓarna
- Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila, Birgediya Janar Effie Defrin ya ce sun tarwatsa duka makaman, babu wanda ya samu rauni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Isra'ila - A ci gaba da musayar wuta da ke ƙara dagula yanayin tsaro a Gabas ta Tsakiya, Iran ta harba makamai masu linzami guda 30 a kan ƙasar Isra’ila.
Jamhuriyar musulunci ta Iran ta harɓa waɗannan makamai masu haɗari ne a cikin harin dare sau biyu yayin da faɗanta da Isra'ila ke ƙara tsananta.

Source: Twitter
Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila (IDF), Birgediya Janar Effie Defrin, ya tabbatar da lamarin, kamar yadda jaridar Israel Times ta rauwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun tare makaman da Iran ta harɓa Isra'ila
A cewarsa, sojoji sun samu nasarar tarwatsa galibin waɗannan makamai masu linzami tun a sararin sama ta hanyar na’urorin tsaron iska na Isra’ila.
Kakakin sojojin ya kuma bayyana cewa ba a samu wanda ya jikkata ko ya mutu ba sakamakon sabon harin Iran.
“Iran ta harbo makamai kusan 30 cikin dare a hare-hare biyu. Rundunar soji ta yi aiki tukuru wajen kawar da barazanar, kuma mun yi nasarar tare mafi yawansu ba tare da wani rauni ko asarar rai ba,”
- Inji Janar Defrin.
Abin da ya faru a sabon harin da Iran ta kai
Harin ya faru ne cikin daren ranar Laraba, inda rahotanni suka bayyana cewa an ji ƙarar fashe-fashe a sassan Isra’ila, musamman a Arewa da tsakiyar ƙasar.
Isra’ila na da tsarin kariya daga makamai da ya haɗa da Iron Dome, David’s Sling da Arrow missile defense systems, waɗanda aka tsara musamman domin kare ƙasar daga hare-haren makamai masu linzami.
Wasu daga cikin makaman da Iran ta harbo a wanna nkaron, an dakile su tun kafin su tsallaka ko su sauka kan gine-gine a Isra’ila.

Source: Getty Images
Sojojin Isra'ila sun ce a shirye suke
Ko da yake ba a samu raunuka ba, wannan hari ya sake bayyana girman rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila, wanda har yanzu ba a ga wani sauƙi ko mafita na diflomasiyya ba.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana nan daram a cikin shirin ko-ta-kwana domin kare jama'a da ƙasar gaba ɗaya kamar yadda Punch ta rahoto.
Iran ta aika saƙon gargaɗi birnin Haifa
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta gargaɗi mazauna birnin Haifa na Isra'ila su gaggauta tashi su fice daga garin tun kafin lokaci ya ƙure masu.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan hare-haren da Iran ta kai wa yankin.cikin makon nan, wanda ya lalata muhimman wurare a birnin Haifa.
Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta shida da ɓarkewar yaƙi tsakanin Iran da Isra'ila, ƙasashen da suka jima ba su ga maciji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

