"Yaƙi Ya Kara Zafi": Iran Ta Sake Tunkarar Isra'ila, Ta Aika Saƙo ga Mutanen Birnin Haifa
- Ƙasar Iran ta gargaɗi mazauna birnin Haifa na Isra'ila su gaggauta tashi su fice daga garin tun kafin lokaci ya ƙure masu
- Wannna gargaɗi na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Firaministan Isra'ila, Benjamin Natanyahu ya gargaɗi mutanen Tehran su fice daga birnin
- A kwanakin baya Iran ta kai hare-hare birnin Haifa, inda ta lalata wata matatar man Isra'ila da wasu muhimman wurare
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin ƙasar Iran ta bukaci mazauna birnin Haifa da ke Isra’ila da su fice daga garin domin kare rayukansu daga hatsarin da ke tafe.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan hare-haren da Iran ta kai wa yankin cikin makon nan, wanda ya lalata muhimman wurare a birnin.

Source: Getty Images
Rahoton BBC Hausa ya ce duk da yake hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa an dakile mafi yawan makaman da Iran ta harba, wasu daga cikinsu sun faɗo cikin birnin tare da jefa mutane cikin fargaba.

Kara karanta wannan
Shirin nukiliya: Iran ta gamu da babbar matsala a yaƙin da take yi da ƙasar Isra'ila
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haren-haren da Iran ta kai birnin Haifa
Idan za ku iya tunawa, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa matatar man fetur da ke birnin Haifa ta daina aiki sakamakon hare-haren roka da Iran ta ƙaddamar.
Hukumar da ke kula da matatar mai a Haifa ta ƙasar Isra’ila, ta sanar da dakatar da dukkan ayyukanta bayan wani harin roka da Iran ta kai.
Kamfanin Bazan Group, wanda ke kula da harkokin gudanar da matatar, ya bayyana cewa harin ya tilasta musu rufe ayyuka gaba ɗaya,
Bayan haka, rahotanni sun nuna cewa hare-haren Iran sun kuma lalata wasu sansanonin sojin Isra'ila bayan matatar man feturin Haifa.
Mutanen Isra'ila sun fara guduwa daga gidajensu
Hakan ya sa yahudawa suka fara guduwa daga gidajensu domin neman tsira daga haɗarin makaman da Iran ke harbawa kan ƙasarhu.
An tattaro cewa yahudawa sun gudu sun koma tashoshin jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa da ke Isra'ila don kare kansu.

Kara karanta wannan
Isra'ila: Iran ta umarci jama'a su daina amfani da whatsApp, ta fadi sharrin manhajar
Sai dai yayin da yaƙin ke ƙara ta'azzzara tsakanin ƙasashen biyu, Iran ta aika saƙon gargaɗi ga mazauna birnin Haifa.

Source: Getty Images
Iran ta aika saƙon gargaɗi ga mazauna Haifa
Jamhuriyar musulunci ta Iran ta buƙaci duka fararen hular da ke zaune a birnin Haifa na ƙasar Isra'ila su gaggauta ficewa daga garin dom tsira da rayukansu.
A kwanakin bayan Firaministan Isra'ila ya yi makamancin irin wannan gargaɗi ga mutane Tehran, babban birnin Iran, inda ya nemi su fice daga garin tun da wuri.
A yau Laraba, 18 ga watan Yuni, 2025 aka shiga rana ta shida da fara musayar wuta tsakanin Isra'ila da Iran, wanda kawo yanzu aka rasa rayukan ɗaruruwan mutane.
Iran ta buƙaci ƴan kasar su goge Whatsapp
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Iran, ta hannun gidan talabijin dinta, ta umarci ƴan kasar da su cire manhajar WhatsApp daga wayoyinsu saboda tsaro.
Ana zargin manhajar na tattara bayanan masu amfani da ita domin aika su zuwa kasar Isra’ila yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin kasashen biyu.
Sai dai Kamfanin Meta ya nuna damuwa game da yunkurin hukumomin Iran na hana amfani da manhajar WhatsApp a fadin kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng