Iran Ta Kara Kai Zafafan Hare Hare, Ta Harba Makamai Masu Linzami kan Isra'ila
- Ƙasar Iran ta sanar da ƙara kai hare-hare Isra'ila yayin da rikici tsakanin kasashen biyu ke ƙara ta'azzara
- A wata sanarwa da gidan talabijin na gwamnatin Iran ya fitar, ta ce ƙasar ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami
- Har yanzu babu wata sanarwa daga Isra'ila kan waɗannan hare-hare da Iran ta tabbatar da kai wa a yau Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Ƙasar Iran ta ƙaddamar da wani sabon jerin hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami kan Isra’ila.
An ruwaito cewa wannan shi ne zai zama karo na 10 a jerin hare-haren soji da ƙasar Iran ta kai Isra'ila wanda ta sanya wa suna “Operation Honest Promise 3."

Source: Twitter
Gidan talabijin na gwamnati a Tehran, babban birnin Iran ne ya tabbatar da kai sababbin hare-haren, kamar yadda tashar DW ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙasar Iran ta kai sababbin hare-hare a Isra'ila
An tabbatar da hare-haren na baya-bayan nan a ranar Talata, 17 ga watan Yuni, 2025 a daidai lokacin da rikicin tsakanin ƙasashen biyu ya shiga rana ta biyar a jere.
Gidan talabijin na gwamnatin ya bayyana cewa Rundunar Musulunci ta Iran (IRGC) ce ta jagoranci kai sababbin hare-haren, wadanda ta ce an kai su ne kan biranen Isra'ila.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da kusanci da gwamnatin Iran, shi ma ya tabbatar da an kai waɗannan sababbin hare-hare.
Makaman da Iran ta yi amfani da su
Rahoton ya kara da cewa a wannan karon, Iran ta harba jirage marasa matuƙa da rokoki duk a wani bangare na ramuwar gayya da Iran ke ci gaba da yi.
Tun farko dai Isra'ila ta fara kai hari Iran, inda ta kashe manyan hafsoshin soji da masana nukiliya, tare da ɗaruruwan fararen hula.
Bayan haka ne Iran ta fara kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila, ita ma ta kashe mutane sama da 20, rahoton CNN.

Source: Getty Images
Wane illa hare-haren Iran suka yi wa Isra'ila?
A halin yanzu dai babu wata sanarwa kai tsaye daga hukumomin Isra’ila kan sababbin hare-haren da Iran ta ce ta kai.
Sai dai wadannan hare-haren na kara dagula rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila, yayin da manyan ƙasashe. duniya da yankin Gabas ta Tsakiya ke sa ido sosai kan lamarin.
Har kawo yanzu ba a tantance yawan barnar da hare-haren suka haddasa ko adadin asarar rayuka ba.
Iran ta lalata wata matatar man Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar da ke kula da matatar mai a Haifa ta ƙasar Isra’ila, ta sanar da dakatar da dukkan ayyukanta bayan wani harin roka da Iran ta kai.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta samu nasarar lalata muhimman ɓangarori a matatar, lamarin da aya tilastawa kamfanin da ke kula da ita dakatar da aiki.
Kamfanin ya ce rokokin da Iran ta harba sun lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da ita wajen sarrafa man fetur.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

