Air India: Jirgin Sama Ɗauke da Mutane Sama da 200 Ya Gamu da Mummunan Hatsari

Air India: Jirgin Sama Ɗauke da Mutane Sama da 200 Ya Gamu da Mummunan Hatsari

  • Jirgin sama na kamfanin Air India ya gamu da hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga birnin Ahmedabad da nufin zuwa Landan
  • Hukumomin ƙasar India sun tabbatar da cewa jirgin na ɗauke da mutane 242 lokacin da ya faɗo yau Alhamis, 12 ga watan Yuni, 2025
  • Kamfanin Air India ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni aka kafa cibiyar tuntuɓa ta gaggawa domin sanar da iyalai halin da ake ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

India - Wani jirgin fasinja mallakin kamfanin Air India da ke kan hanyarsa ta zuwa London Gatwick ya gamu da mummunan hatsari ranar Alhamis.

Jirgin saman wanda aka ce yana ɗauke da mutane 242 ya yi hatsari ne a birnin Ahmedabad na yammacin ƙasar Indiya.

Jirgin Air India ya yi hatsari.
Jirgin sama ɗauke da fasinjoji sama da 200 ya faɗo ƙasa a India Hoto: @airindia
Source: Twitter

BBC ta rahoto cewa jirgin, mai lamba AI171, nau’in Boeing 787-8 Dreamliner, ya rikito ƙasa ne jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na birnin Ahmedabad.

Kara karanta wannan

Ana murnar ranar dimokuradiyya, Peter Obi ya sake dura kan gwamnatin Tinubu

Ministan harkokin sufurin jiragen sama na Indiya, Ram Mohan Naidu Kinjarapu, ya bayyana cewa yana cikin “zullumi da ɓacin rai” bisa wannan hatsari.

Yadda jirgin sama na Air India ya yi hatsari

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Indiya (DGCA) ta bayyana cewa:

“Jirgin ya turo da sakon gaggawa kafin ya faɗi a wajen filin jirgin sama.”

Tashar CNN ta bayyana cewa an ga hayaki ya turnuƙe sararin sama, yana tasowa daga inda hatsarin ya faru.

Rahoto ya nuna cewa mutanen da ke cikin jirgin saman sun ƙunshi fasinjoji 230, ma’aikatan 10 da matuƙa biyu.

Birnin Ahmedabad, babban birnin jihar Gujarat, yana da yawan jama’a kusan miliyan takwas kuma filin jirgin saman yana kewaye da gidajen mutane sosai.

Wane mataki hukumomin India suka ɗauka?

Ministan jiragen saman India, Ram Mohan Naidu Kinjarapu ya umurci dukkan hukumomin jin kai da na sufurin jiragen sama da su haɗa kai su nufi wurin da hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

Miyagu sun farmaki bayin Allah a Plateau, an kashe mutane

"An tura tawagar ba da agajin gaggawa. Muna iya bakin ƙoƙarin mu wajen tabbatar da cewa duk wasu kayayyakin bayar da agaji na lafiya sun isa wurin a kan lokaci," in ji shi.
Hatsarin jirgi a India.
Jirgin Air India ɗauke da mutane.242 ya faɗo bayan tashinsa a Ahmedabad Hoto: @homelander
Source: Twitter

Kamfanin Air India ya tabbatar da lamarin

Shugaban kamfanin sufurin Air India, Natarajan Chandrasekaran, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce:

“Cikin alhini da takaici, ina tabbatar da cewa jirgin Air India Flight 171 da ya tashi daga Ahmedabad zuwa London Gatwick ya gamu da wani mummunan hatsari a yau.
"Muna mika ta’aziyyarmu da alhini ga dukan iyalai da masoyan waɗanda abin ya shafa a cikin wannan mummunan lamari.”

Chandrasekaran ya ƙara da cewa an kafa cibiyar tuntuɓar gaggawa da tawagar agaji domin bai wa iyalai bayanai kan halin da ake ciki.

Ƙaramin jirgi ya yi hatsari a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin sama kirar Cessna 550 Citation ya faɗo a cikin garin San Diego da ke ƙasar Amurka.

Rahotanmi sun nuna cewa jirgin ya faɗo ne a lokacin da hazo ya lullube sararin samaniya, lamarin da ya haddasa ƙonewar gidajen mutane da dama.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasar Amurka (FAA) ta ce ba a tabbatar da yawan mutanen da ke cikin ƙaramin jirgin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262