Kasashe 5 ba Su ga Watan Babbar Sallah ba, Sun Ayyana Asabar Matsayin Ranar Idi

Kasashe 5 ba Su ga Watan Babbar Sallah ba, Sun Ayyana Asabar Matsayin Ranar Idi

Babbar Sallah (Eid Al Adha), watau sallar layya, na daya daga cikin manyan bukukuwa a Musulunci, wanda ke tunawa da sadaukarwar Annabi Ibrahim wajen yarda da umarnin Allah na yanka ɗansa.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A shekarar 2025, wasu kasashe za su gudanar da bikin babbar Sallah ne a ranar 6 ga Yuni, yayin da wasu za su yi tasu hawan sallar a ranar 7 ga Yuni.

Sakamakon rashin ganin wata, wasu kasashe 5 za su yi babbar Sallah a ranar Asabar, 7 ga Yuni
Na'urorin da ake amfani da su domin ganin jinjirin wata a Saudiyya. Hoto: @HaramainInfo
Source: Twitter

Ga bayani dalla-dalla na dalilan da suka haddasa bambancin ranakun hawan sallar layya a kasashe.

1. Kalandar wata na jawo bambancin ranar

Ana gudanar da sallar Layya ne a ranar 10 ga watan Dhul-Hijjah na kowace shekara, wato wata na 12 a kalandar Musulunci.

Saboda Musulunci na amfani da tsarin ganin wata wajen lissafin kwanaki, hakan ya kan sa watan Musulunci ya zama mai kwanaki 29 ko 30 bisa ga bayyanar jinjirin wata.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Za a raba dubban shanun layya kyauta ga Musulmi a Kano, Abuja da jihohi 10

Wannan ya sa bukukuwan Musulunci ke raguwa da kusan kwana 10 zuwa 11 duk shekara a kalandar Gregorian, watau kalandar Miladiyyar haihuwar Annabi Isah dan Maryama.

A 2025, watan Dhul-Hijjah ya fara ne a ranar 28 da 29 ga Mayu, wanda ke nuni da cewa babbar Sallah za ta kasance a ranar 6 ko 7 ga Yuni, ya daganta da ganin wata na kasar.

2. Tsarin ganin wata ya bambanta a kasashe

Babban dalilin bambancin rana shi ne tsarin ganin wata da kowace kasa ke bi, kamar yadda rahoton Gulf News ya bayyana.

Kasar Saudiyya da UAE, Qatar, Oman da Australia na amfani da tsarin haɗa ganin wata da ido da kuma lissafin ilimin taurari, kuma sun tabbatar da cewa babbar Sallah za ta kama a ranar 6 ga Yuni bisa ga ganin wata a ranar 27 ga Mayu.

Amma kasashe kamar India, Pakistan, Bangladesh da Morocco na gudanar da nasu zaman ganin watan, kuma an ce sun ga jinjirin ne a ranar 28 ga Mayu, wanda hakan ya sa za su yi Sallah a ranar 7 ga Yuni.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

3. Tasirin Saudiyya a matsayin kasar aikin Hajji

Kamar yadda Saudiyya ke karɓar alhazai, tana taka muhimmiyar rawa wajen ayyana ranar hawan babbar Sallah, a kasashe da dama.

Ranar Arafa – wata rana mai muhimmanci ga aikin Hajji – za ta kasance a ranar 5 ga Yuni, sannan a yi hawan babban Sallah a ranar 6, bisa kalandar Umm al-Qura.

Kasashen Gulf da dama na bin kalandar Saudiyya don daidaito da masu gudanar da aikin Hajji, amma kasashe kamar Pakistan da India na fifita gani wata a kasashensu.

4. Sassaucin al’ada da addini

Duk da bambancin ranar da aka samu, ma’anar babbar Sallah bai canja ba: zuwa sallar idi, yanka dabba (layya), da raba nama ga dangi, makwabta da mabukata.

Ko ranar 6 ko 7 aka yi ta, bikin na jaddada imani, sadaka da haɗin kai. Wannan sassauci na nuna irin yanda addinin Musulunci ke girmama bambancin al’adu da lokaci.

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan babbar Sallah a Najeriya
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ayyana ganin jinjirin watan Dhul Hijja. Hoto: Getty Iimages
Source: Getty Images

Kasashe 5 da za su yi babbar Sallah ranar 7 ga Yuni

Kara karanta wannan

2027: Sanatoci sun gano dalilin kara karfin Boko Haram da sauran 'yan ta'adda

Pakistan:

Hukumar Ruet-e-Hilal ta kasa ta tabbatar da cewa ba a ga wata ba, wanda ya sa Dhul-Hijjah zai fara a ranar 29 ga Mayu, Sallah a ranar 7 ga Yuni a cewar rahoton Hindustan Times.

Malaysia:

Hukumar ganin wata ta Malaysia ta sanar da rashin ganin wata, don haka babbar Sallah za ta kasance a ranar 7 ga Yuni.

Brunei:

Ita ma kasar Brunei ta bi sahun Malaysia, inda ta sanar da gudanar da sallar layya a ranar 7 ga Yuni.

India:

Bisa ga ganin wata a yankuna daban-daban, ana sa ran za a yi babbar Sallah a ranar 7 ga Yuni a yawancin sassan ƙasar.

Bangladesh:

Za a sanar da ranar Sallah a daren Laraba. Sai dai gwamnati ta riga ta ware hutun Sallah daga 5 zuwa 14 ga Yuni.

An fadi ranar babbar Sallah a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a Najeriya, wanda ya nuna ƙarshen watan Dhul Qa'adah a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yadda aka samu 'dan sandan da aka kashe a Kano da hannu a kisan 'barayin kaji' tun 2021

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bayyana ranar Laraba, 28 ga Mayu, a matsayin farkon watan Dhul Hijjah na shekarar Hijira 1446.

Wannan na nufin cewa za a gudanar da babbar Sallah (Eid al-Adha) a Najeriya a ranar Juma'a, 6 ga watan Yuni, 2025, kamar yadda Musulmi za su hau idi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com