Nahiyar Afirka Ta Yi Babban Rashi, Fitaccen Marubuci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Naniyar Afirka ta yi babban rashi da fitaccen marubuci ɗan kasar Kenya, Ngũgĩ wa Thiong’o ya riga mu gidan gaskiya
- An ruwaito cewa marigayin wanda ya sha gwagwarmaya a rayuwa ya mutu ne ranar Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025 yana da shekaru 87
- Marigayin ya rubuta litattafai da dama a rayuwarsa, inda ake ganin babu kamarsa a marubutan Gabashin nahiyar Afirka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kenya - Fitaccen marubucin nan ɗan ƙasar Kenya, Ngũgĩ wa Thiong’o, ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.
Rahotanni daga iyalansa sun nuna cewa marigayin ya riga mu gidan gaskiya ne a jiya Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025.

Source: Twitter
A daren Laraba, diyarsa Wanjiku wa Ngugi ta wallafa sanarwar rasuwarsa a shafinta na Facebook, inda ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Cikin yanayi mai cike da kewa muke sanar da rasuwar mahaifinmu, Ngũgĩ wa Thiong’o, a safiyar Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025.”
An faɗi burin futaccen marubucin na karshe
Wanjiku ta bayyana irin rayuwar da mahaifinta ya yi da kuma burinsa na karshe:
“Ya yi rayuwa mai kyau kuma ya yi gwagwarmaya mai kyau. Kamar yadda ya bukata kafin rasuwarsa, za mu yi murnar rayuwarsa da ayyukan da ya yi. Rayuwa mai albarka, karshe mai albarka."
Ta ce nan bada jimawa ba, mai magana da yawun iyalinsu, Nducu wa Ngugi, zai fitar da cikakkun bayanai kan bukin tunawa da marigayin da jana'izarsa.
Ngũgĩ: Gwarzon adabin Afirka
An haifi Ngũgĩ a ranar 5 ga Janairu, 1938. Ya wallafa litattafai da dama ciki har da Weep Not Child, The River Between, Petals of Blood, da Wizard of the Crow.
Ya shahara a matsayin marubuci mai tsantsar salo na adabin Afirka, tare da kirkirar litattafan yara da kuma bayyana rashin jin dadinsa kan rashin daidaito da zalunci a cikin al’umma.

Kara karanta wannan
Malamin addini ya fito karara ya gayawa Tinubu abin da zai hana shi tazarce a 2207
Ana ganin marigayi Ngũgĩ a matsayin babban jigon marubutan Gabashin nahiyar Afirka, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Source: Facebook
Nasarori da kalubalen da ya fuskanta
Ya kafa mujallar Mutiri a harshen Gikuyu, kuma daya daga cikin gajerun labaransa 'The Upright Revolution: Or Why Humans Walk Upright', an fassara shi zuwa harsuna 100 a fadin duniya.
Ko da yake ya fuskanci dauri da gudun hijira saboda suka da ya yi wa gwamnatin kama-karya a Kenya, Ngũgĩ ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin fitattun a adabin Afirka.
A watan Maris na 2024, aka samu labarin cewa marigayin na fama da matsananciyar cutar ƙoda kuma yana rayuwa shi kaɗai tare da kulawar jami’an lafiya a gidansa da ke California a Amurka.
Shugaban ƙasa mafi talauci a duniya ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasar Uruguay wanda a zamaninsa ake kiransa da 'shugaba mafi talauci a duniya', José Mujica ya rasu.
An ruwaito cewa ana kiran Pepe a matsayin shugaban ƙasa mafi talauci a duniya ne saboda yadda yake tafiyar da rayuwarsa cikin sauƙi, irin ta talakawa.
Marigayi Pepe ya shugabanci Uruguay daga 2010 zuwa 2015 kuma ya shahara da saukin rayuwarsa, ya ƙi da rayuwa ta almubazzaranci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
