Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa, Ta Bayyana Ranakun Hawa Arafah da Babbar Sallah
- Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a yau Talata, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1446 daidai da 27 ga watan Mayu
- A sanarwar da hukumomin suka fitar da yammacin nan, za a yi hawan Arafah a ƙasar a ranar Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2027
- Haka nan kuma musulmi a ƙasar Saudiyya za su yi hawan idin layya watau Eid El Adha ranar Juma'a, 10 ga watan Dhul Hijjah daidai da 6 ga watan Yuni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a yau Talata, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1446H daidai da 27 ga watan Mayu, 2025.
Hakan dai na nufin gobe Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025 zai kama 1 kenan ga watan Dhul Hijjah, 1446H, wata na 12 a jerin watannin kalandar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan
Eid El Adha: Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da ranar babbar sallah a Najeriya

Source: Twitter
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukumar kula da manyan masallatai biyu masu daraja da alfarma Inside The Haramai a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ranakun Arafah da babbar sallah a Saudiyya
A cewar sanarwar, alhazai za su yi hawan Arafah a ranar Alhamis, 9 ga watan Dhul Hijjah, wanda zai yi daidai da 5 ga watan Yuni, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa sallar layya watau Eid El Adha za ta kama ranar 6 ga watan Yuni, 2025 daidai da 10 ga watan Dhul Hijjah, 1446H.
Wannan wata na Dhul Hijjah na da matuƙar daraja da ƙima a addinin musulunci, a cikinsa ne musulmi ke yin ibadar aikin hajji, ɗaya daga cikin rukunan addinin.
Haka zalika a wannan wata ne musulmi daga kowane yanki a duniya suke yin sallar layya, watau babbar sallah (Eid El Adha), ɗaya daga cikin idi biyu da musulmai ke yi a kowace shekara.

Source: Facebook
Sanarwar da Saudiyya ta fitar kan ganin wata
Sanarwar da hukumomin Saudiyya suka fitar ta ce:
"An ga jinjirin wata a Saudiyya, gobe Laraba, 28 ga watan Mayu, 2027 za ta kama 1 ga watan Dhul Hijjah, 1446H.
"Ranar hawa Arafah kuma za ta kama ranar Alhamis, 9 ga watan Dhul Hijjah, 1446 wanda zai zama daidai da 5 ga watan Yuni, 2025.
"Sai kuma Eid El Adha watau sallar layya, ita kuma za a yi hawan idin a ranar Juma'a ta makon gobe, 6 ga watan Yuni, 2025 daidai 10 ga watan Dhul Hijjah.
Wannan sanarwa dai ta tabbatar da cewa watan Dhul Qa'adah ya kare daga yau Talata, sannan gobe Laraba ne 1 ga watan Dhul Hijjah, 1446H.
Kasar Saudiyya ta naɗa limamin Arafah
A wani labarin, kun ji cewa hukumomi a Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid ne zai yi huɗuba a tsayuwar Arafah ta shekarar 1446 bayan Hijira.
Sheikh Saleh zai gabatar da huɗubar wannan rana mai matuƙar daraja ta Arafah daga masallacin Namira a ranar Alhamis, 9 ga watan Dhul Hijjah, 1446H.
Malamin ya rike mukamai da dama a Saudiyya, ciki har da shugaban majalisar Shura a shekarar 1422 da shugaban babban kotun shari’a a 1430.
Asali: Legit.ng

