Falasdinawa Sun Samu Goyon Baya a Duniya, Birtaniya ta Raba Hanya da Isra'ila
- Gwamnatin Birtaniya ta dakatar da tattaunawa kan yarjejeniyar cinikayya da Isra’ila saboda yadda kasar ke tafiyar da yakin Gaza
- Sakataren harkokin wajen Birtaniya ya bayyana karin takunkumi kan masu zaune a haramtattun wurare a yankin West Bank
- Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya soki yadda Isra’ila ke jefa yaran Gaza cikin wahala, yana mai kira da a tsagaita wuta nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Britain - Gwamnatin Birtaniya ta sanar da dakatar da tattaunawa kan yarjejeniyar cinikayya da Isra’ila sakamakon yadda gwamnatin Isra’ila ke gudanar da yakin da ta ke yi a Gaza.
Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da dubban Falasdinawa ke fuskantar ruwan bama-bamai, hare hare ta ƙasa da kuma yunwa da ke kara ta’azzara halin da suke ciki.

Source: Getty Images
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ne ya bayyana hakan a gaban majalisar dokokin kasar a ranar Talata
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
David Lammy ya kuma ayyana karin takunkumi kan wasu masu zaune a haramtattun wurare na West Bank.
Birtaniya ta sakawa Yahudawa takunkumi saboda Gaza
Lammy ya ce gwamnatin Birtaniya ta dauki matakin ne duba da yadda Isra’ila ke cigaba da nuna halin ko-in-kula da rikicin yankin, wanda ke barazana ga 'yancin Falasdinawa.
CNN ta rahoto ya ce:
"Mun kara takunkumi kan wasu mutane uku, wuraren zama biyu da kungiyoyi biyu da ke tallafa wa tashin hankali kan al’ummar Falasdinu."
A cewarsa, duk da cewa yarjejeniyar cinikayya da Isra’ila da aka kulla a baya tana nan, ba za su cigaba da tattaunawa ba muddin Isra’ila tana aiwatar da munanan manufofi a Gaza da West Bank.
Firaministan Birtaniya ya gargadi kasar Isra'ila
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya kara matsa lamba a kan Isra’ila, inda ya ce irin halin da yaran Gaza ke ciki abin takaici ne matuka.

Kara karanta wannan
2027: APC ta dauki zafi da Atiku ya ambato mutanenta cikin masu son kifar da Tinubu
A cewarsa:
“Ba za a lamunci wannan wahala da yara ke ciki ba. Na sake nanata bukatar tsagaita wuta domin kare rayuka.”
Lammy ya ce Ministan harkokin Gabas ta Tsakiya na Birtaniya zai isar da sako kai tsaye ga jakadiyar Isra’ila a Birtaniya cewa toshe hanyoyin agaji da aka yi tsawon mako 11 abin kunya ne.

Source: Facebook
Kasashe sun fara daukar mataki kan Isra'ila
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta kada kuri’ar nazari kan yarjejeniyar hadin gwiwar kasuwanci da Isra’ila, kamar yadda shugaban harkokin diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta sanar.
Haka kuma, a ranar Litinin, kasashen Birtaniya, Faransa da Kanada sun hadu wajen caccakar yadda Isra’ila ke tafiyar da yakin da kuma hare-haren da take kaiwa a West Bank.
Fafaroma ya yi magana kan zaman lafiya a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa sabon Fafaroma da ya sha rantsuwa a ranar Lahadi da ta gabata ya yi magana kan zaman lafiya.

Kara karanta wannan
A ƙarshe, Birtaniya ta tsoma baki kan tsare tsaren tattalin arzikin Tinubu a Najeriya
Fafaroma Leo XVI ya bukaci kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin zirin Gaza da kasar Ira'ila ke kai hare hare.
Haka zalika Fafaroman ya bukaci yin sulhu game da yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha da ya shafi kasashe da dama a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
