"Kudin Haya, N18m": Ƴar Najeriya Ta Fadi Miliyoyin da Ta Ke Kashe wa a Birtaniya

"Kudin Haya, N18m": Ƴar Najeriya Ta Fadi Miliyoyin da Ta Ke Kashe wa a Birtaniya

  • Wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar Birtaniya ta bayyana yadda take kashe makudaden kudade a kone wata
  • Ta bayyana cewa tana zaune ita kaɗai a ɗakin haya na mutum guda, inda kuɗaɗen da take kashewa suke kai £988 (fiye da Naira miliyan 2)
  • Ma'abota soshiyal midiya sun tambayi garin da take da zama a Birtaniya da har take kashe makudan kudi a hayar gida, wutar lantarki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Birtaniya - Wata matashiya ‘yar Najeriya mai shekara 25 da ke zaune ita kaɗai a Birtaniya ta bayyana kuɗin da take kashewa a kowane wata.

A cewar matashiyar, kudin da take kashe wa duk wata ya kai kusan £988 (fiye da Naira miliyan 2), lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

'Yar Najeriya ta bayyana kudaden da take kashe wa duk wata a Birtaniya.
'Yar Najeriya mazauniya Birtaniya, ta bayyana kudin da take kashewa duk wata. Hoto: @dewdailyy
Asali: TikTok

Budurwa ta fadi nawa take kashe wa a Birtaniya

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta hukunta matashin da ya yi yunkurin cakawa mahaifinsa makami

Budurwar mai amfani da sunan @dewdailyy a TikTok, ta ce tana zaune ne a gidan haya, amma ba ta bayyana jihar da ke zaune a Birtaniya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwar ta lissafa kuɗaɗen da take kashewa, wanda ya haɗa da kudin hayar gida £725 (kimanin Naira miliyan 1.5), da kudin harajin ƙaramar hukuma £107 (kimanin N223,000).

Sauran kudaden da take kashewa sun hada da kudin wutar lantarki £95 (kimanin N198,400), kudin intanet £29 (kimanin N60,500), kudin ruwa £22 (kimanin N45,900), da kudin wayar salula £10 (kimanin N20,800)

Dewdailyy ta ƙara da cewa gaba ɗaya kuɗin da take kashewa a kowane wata a Birtaniya ya na kai £988 ko ya haura hakan (fiye da Naira miliyan 2).

Kalli bidiyon TikTok ɗinta na ƙasa:

Watch on TikTok

Martanin jama’a kan kuɗin da take kashewa

sinachi247:

"Nawa ki ke samu? Za ki iya yin bidiyo game da yadda kike tafiyar da kuɗin da kike samu da kashewa? Na gode."

Kara karanta wannan

Tirƙashi: Saudiyya na barazanar ɗaure alhazan Najeriya da wasu ƙasashe kan Umrah

Melanielocs:

"Shi ya sa zan fi son kama haya tare da wasu. Abin da kawai ba zan iya haɗawa da wasu ba shi ne dakin dafa abinci da kuma bandaki."

redz_646:

"Ba wai ina titsiye ki ba ne, za ki iya faɗin unguwar ko kamfanin da ke da gidan? Wataƙila wani zai amfana da wannan. Na gode."

LeloVatiswa

"Ni ɗalibar jami’a ce kuma ina biyan £300 a matsayin kudin hayar ƙaramin ɗakin da nake zama a London. Ina jin kamar in fashe da kuka."

MoNextAlakija:

"Duk wata-wata? Ni dai ina matukar jin takaicin biyan kudin haya duk wata, na fi son na shekara."

Elizabethnusi ta ce:

"Ehhnn ɗakin haya daya a kan £725 😱 don Allah wane gari ne wannan?"

shobydprodigy:

"Fada garin da kike, kada kawai ki ce Birtaniya, wani na Hull, wani na Landan, duka a UK su ke amma tsadar rayuwarsu daban ne."

Matsakaicin kuɗin rayuwa a Birtaniya

Kara karanta wannan

Rogo ya jawo 'dan shekaru 49 ya sassara mahaifiyarsa da adda har barzahu

Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ke kashe makudan kudi duk wata a zaman da take yi Birtaniya
Wata 'yar Najeriya da ke rayuwa a Birtaniya a wani gidan haya da take biyan N1.5m duk wata. Hoto: @Dewdailyy
Asali: TikTok

A cewar rahoton UKGIC, matsakaicin kuɗin haya na ɗakin mutum daya a Birtaniya ya kai £1,800 (N3,812,875.20) a wata, abin da ke nuna cewa budurwar ta samu rangwamen haya sosai.

Haka kuma, a wurare irin su Manchester da Birmingham, ana biyan kudin haya tsakanin £800 (N1,694,611.20) zuwa £1,100 (N2,330,090.40) a kowane wata.

Amma ya kamata a lura cewa ba ta bayyana garin da take zaune a ƙasar Birtaniya ba, don haka ba za a iya gasgatawa ko inkarin abin da take biyan kai tsaye ba.

Game da sauran bukatu kamar wuta, da ruwa, matsakaicin kuɗi biyan wadannan yana kai daga £150 (N317,850.60) zuwa £200 (N423,800.80).

Kuɗin ruwan da budurwar ke biya ya kai £22 (N46,618.09) sai kuma wuta £95 (N201,305.38), abin da ke nuna cewa ba ta kashe kudi kan su sosai ba.

'Yar Najeriya a Birtaniya na neman taimako

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Omolola Bowoto, wata ɗalibar Najeriya da ke karatun digiri na biyu a Jami’ar Essex, Ingila, na neman taimakon al’umma don cigaba da karatu.

Kara karanta wannan

"Ya ɗauka ni ne," Abin da ya faru da ɗiyar Buba Galadima ta kira Tinubu a wayar salula

Ɗalibar na fuskantar barazanar katsewar karatunta idan ta kasa biyan kuɗin makaranta da ya kai £20,700 (sama da Naira miliyan 23.7), a shekararta ta biyu.

Bowoto ta bayyana cewa ta riga ta tara £5,300 (kimanin Naira miliyan 6), amma har yanzu tana buƙatar £15,400 (Naira miliyan 17.6) don kammala biyan bashin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng