Azumi 30: Abin da Ya Sa ba Zai Yiwu a ga Jinjirin Watan Shawwal a Ranar Asabar ba

Azumi 30: Abin da Ya Sa ba Zai Yiwu a ga Jinjirin Watan Shawwal a Ranar Asabar ba

  • Binciken masana falaki ya nuna cewa ba zai yiwu a ga jinjirin watan Shawwal bayan faduwar rana a ranar Asabar, 29 ga Maris ba
  • Rashin iya ganin jinjirin na da nasaba da matsalolin yanayi, warwatsewar haske, da tasirin zafi, wanda ke hana hasken jinjiri bayyana a samaniya
  • Da wannan masana ke ganin cewa, 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446 AH zai kasance ne a ranar Litinin, 31 ga watan Afrilu, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jordan - Ana fargabar cewar ba za a iya ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar, 29 ga watan Maris, a Jordan, sauran kasashen Larabawa ba.

Dr. Ammar Al-Sakaji, shugaban kungiyar ilimin sararin samaniya ta Jordan, ya ce mafi yawan cibiyoyin ilimin taurari na Larabawa da na duniya sun amince da ingantattun bayanan ilimin falaki game da jinjirin watan Shawwal na shekarar 1446 AH.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa kan duba watan sallar azumi

Masana ilimin Falaki sun yi magana kan ganin watan Shawwal na shekarar 1446 AH.
Rahoto ya yi bayani dalilan da za su hana a iya ganin watan Shawwal, 1446 a ranar Asabar. Hoto: @Insharifain
Asali: Twitter

Ranar da jinjirin watan Shawwal zai hadu

Misali, a babban birnin Jordan, Amman, sabon wata zai fara haɗuwa ne da misalin ƙarfe 1:58 na rana, a ranar Asabar, 29 ga Maris, 2025, inji rahoton Arabia Weather.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin faduwar rana, mahangar jinjirin watan a sararin samaniya zai kasance a kusurwar digiri 1.4, yayin da nisan kusurwar wata da rana yake kan digiri 2.2.

Jinjirin watan zai ci gaba da wanzuwa a sararin samaniya na tsawon mintuna 10, a lokacin yana da awanni 4 da mintuna 56, kuma haskenshi zai kai 0.1%.

Wadannan bayanai sun nuna cewa jinjirin watan zai zamo siriri sosai kuma maras haske a sararin samaniya bayan faduwar rana, wanda zai yi wahala a iya ganinsa a wannan ranar.

Wata ya tsaya amma ido ba zai gan shi ba

Duk da cewa, watan zai fito kuma ya tsaya a sararin samaniya bayan faduwar rana, a ranar Asabar, 29 ga Maris, amma an masana Falaki sun ce ba za iya ganinsa ba.

Kara karanta wannan

Ramadan ya zo ƙarshe, Gwamnatin Tinubu ta bayyana ranakun hutun ƙaramar sallah a Najeriya

Masana Falaki sun yi imani da cewa, idon mutum ko na'urar hangen nesa ba za ta iya ganin jinjirin watan a Jordan da sauran kasashen duniya ba.

Wannan ya dace da ka’idojin ganin jinjirin watan na tarihi da na zamani, kamar ka’idar Babilon, ka’idar Al-Battani, ka’idar Elias, ka’idar Schaefer, ka’idar Dungeon, ka’idar Yallop, ka’idar Allawi, da ka’idar Odeh.

Abin da ya sa ba zai yiwu a ga watan ba

Akwai dalilai na ilimin falaki da na kimiyyar lissafi da ke sa ganin jinjirin watan a ranar Asabar, 29 ga Maris, 2025, ya zama “abu mai wahala,” ciki har da:

1. Rikicewar yanayi

Karuwar nauyin iska: Hasken jinjirin wata yana bi ta cikin wata iska mai danshi a sararin samaniya, wanda hakan ke haddasa gurɓata hoton ganinsa ta na'u'rar telescope.

Sauyin yanayi: Rikicewar iskar sararin samaniya na haddasa saitin daukar hoton ya baci, wanda zai hana ganin jinjirin watan.

Kara karanta wannan

Masu bautar kasa a Najeriya na cikin alheri dumu dumu, Tinubu ya fara biyan N77, 000

2. Warwatsewar haske

Warwatsewar hasken 'Rayleigh': Warwatsewar shuɗin hasken sararin samaniya na rage bambancin jinjirin watan da sararin samaniya, wanda ke sa ganin wata ya yi wahala.

Shanyewar haske: Masana sun ce iskar sararin samaniya tana ɗaukar wasu gajerun igiyoyin haske, wanda ke rage ƙarfin ganin wata.

3. Canjin wuri da na siffa

Abubuwan da ke iya hana a ga jinjirin watan Shawwal na 1446 AH a ranar Asabar
Abubuwan da ke iya hana a ga jinjirin watan Shawwal na 1446 AH a ranar Asabar. Hoto: @Insharifain
Asali: Facebook

Canjin wuri: Hasken jinjirin watan yana iya fuskantar juyawar iska, wanda ke sa ya bayyana a wani wurin da ba nan aka saba ganinsa ba.

Canjin siffa: Jinjirin watan na iya bayyana da siffar da ba ta sa ba, ko kuma ya kasance kamar an shimfiɗe shi, ta yadda ba za a iya tantance shi ba.

4. Rashin karfin launi

Haske mai yawa a lokacin faduwar rana: Wurin da jinjirin wata yake fitowa a sararin samaniya yana da haske sosai, wanda ke hana na'ura ta iya bambance launinsa.

5. Daidatuwar yanayin sararin samaniya

Danshi da tururin ruwa: Wadannan abubuwa na rage bayyanar jinjirin watan kuma su na hana na'ura ta iya ganinsa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Kano: Babban mai taimaka wa Gwamna Abba ya rasu ana azumi

Girgije: Hakazalika, girgije na iya rufe jinjirin wata gaba ɗaya, yana hana a iya ganin sa.

6. Tasirin zafi

Sauyin yanayi: Canjin yanayi na iya haifar da rikicewar hoto saboda sauyin zafi a iskar da ke kadawa a sararin samaniya, wanda zai hana a iya ganin watan.

Za a fara duba jinjirin wata a Saudiyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Saudiyya, UAE, Qatar, da Kuwait, da wasu kasashen Yamma irin su Amurka, Birtaniya, za su fara duban jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar.

Hukumomin wadannan kasashe da wasu da dama za su fara neman jinjirin watan bayan sallar Magribah a daren 29 ga Ramadan 1446 AH, wanda ke daidai da 29 ga Maris, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng