An gina kasa ta farko a sararin Samaniya

An gina kasa ta farko a sararin Samaniya

Wani fitaccen attajiri dan kasar Rasha ya kafa kasa ta farko a sararin samaniya mai suna 'Jamhuriyar Asgardia'

An gina kasa ta farko a sararin Samaniya
An gina kasa ta farko a sararin Samaniya

Wani fitaccen attajiri dan kasar Rasha ya kafa kasa ta farko a sararin samaniya mai suna 'Jamhuriyar Asgardia'. Jaridar newsweek ta kasar Amurka ita ce ta rawaito labarin, tace an gabatar da bikin kafa sabuwar kasar, a ranar 25 ga watan Yunin wannan shekarar, a fadar Hofburg dake garin Vienna, babban birnin kasar Austria.

DUBA WANNAN: WHO ta samar da wani sabon magani da zai ke taimakawa wurin ceto mata masu mutuwa a wurin haihuwa

A lokacin da yake ganawa da manema labarai, hamshakin mai kudin mai suna Igor Ashurbeyli yace, "Mun kafa Jamhuriyar Asgardia, a matsayin kasa ta farko a sararin samaniya. Nan da lokaci kankani, zamu fara gina gidaje da kuma gina manyan birane a duniyar wata."

An sanar da cewa, ba ajima da kafa kasar Asgardia ba, kusan mutane dubu 200 suka nemi shaidar zama 'yan kasar.

A halin yanzu Asgardia ta samu tuta, take, fasfo, yan majalisu, ministoci, kundin tsarin mulki, internet, bankuna, shugaban kasa dama duk wani abu da kowacce kasa ke bukata.

A shekarar 2016 ne, hamshakin mai kudin Ashurbeyli ya dauki alkawarin kafa jamhuriyar Asgardia, inda yace, "Samar da kasar, wani muhimmin cigaba ne a wayewar duniyar mu ta yau."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel