Ana Fargabar Gwamnatin Trump Za Ta Kori 'Yan Najeriya da ke Karatu a Kasar Amurka

Ana Fargabar Gwamnatin Trump Za Ta Kori 'Yan Najeriya da ke Karatu a Kasar Amurka

  • Gwamnatin Donald Trump na iya korar 'yan Najeriya da ke karatu a Amurka idan ta yanke hukuncin kasancewarsu ba ta da amfani ga kasar
  • Najeriya ta zama kasa ta bakwai a duniya, sannan kasa ta daya a Afirka wajen yawan dalibai a Amurka, inda suka kai 20,029 a 2023/2024
  • Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce daliban waje na mamaye guraben karatu a jami’o’in kasar, lamarin da ke tauye damar Amurkawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Gwamnatin Shugaba Donald Trump na iya korar 'yan Najeriya da ke karatu a Amurka idan ta yanke hukuncin kasancewarsu ba ta amfani ga kasar.

A shekarar 2024, Amurka ta samu karin yawan dalibai 'yan kasashen waje, bayan wasu kasashe sun sanya takunkumin biza don rage shigowar baki.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Gwamnatin Trump ta yi magana kan korar daliban da ba su cancanci zama a Amurka ba
Akwai yiwuwar Amurka ta hada har da 'yan Najeriya a daliban da za ta iya kora daga kasar. Hoto: @realDonaldTrump
Asali: Getty Images

Matakin Amurka na barazana ga daliban Najeriya

Rahoton gwamnatin Amurka ya nuna cewa 'yan Najeriya suna daga cikin mafi yawan daliban da suka yi rajistar karatu a kasar, inji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shekarar 2023/2024, Najeriya ta kasance kasa ta bakwai a duniya kuma ta daya a Afirka wajen yawan dalibai a Amurka, inda suka kai 20,029.

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa yawan korar baki zai karu yayin da gwamnatin Trump ke kokarin kawar da baƙin da ke zama ba bisa ka’ida ba.

Da aka tambaye shi ko hakan zai shafi daliban kasashen waje da suka shiga bisa doka, ya amsa da eh.

Trump na da ikon korar mutane daga Amurka

JD Vance ya ce wannan ba batun ‘yancin fadin albarkacin baki ba ne, sai dai batun tsaro da yanke shawarar wadanda suka dace su kasance cikin kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

Mataimakin ya kara da cewa shugaban kasa da sakataren harkokin waje suna da iko na tantance cancantar daliban kasashen waje su ci gaba da zama ko a kore su.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ya amince da cewa adadin korar bakin haure zai iya karuwa, kodayake ba a san yawan su ba tukuna.

Vance ya ce:

“Idan shugaban kasa da sakataren harkokin waje sun yanke hukuncin cewa wani ba shi da hakkin zama a Amurka, sai a kore shi.”

Daliban waje na tauye Amurkawa a karatun jami'a

JD Vance ya yi magana kan yiwuwar korar daliban kasashen waje daga jami'o'in Amurka
Shugaba Donald Trump tare da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance. Hoto: @JDVance
Asali: Twitter

Ya bayyana damuwarsa kan daliban kasashen waje da ke mamaye guraben karatu a manyan jami’o’i, yana mai cewa hakan yana tauye damar Amurkawa.

Vance ya zargi cewa yawancin daliban kasashen waje, musamman na kasar Sin, suna karbar guraben da ya kamata su kasance na Amurkawa.

“Wani dalibi dan Najeriya ko na wata kasa na iya mamaye gurbin karatun wani matashi dan Amurka, wanda zai hana shi samun damar shiga jami’a.”

Kara karanta wannan

Jigawa: Amarya ta watsawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi, ta zama silar ajalinta

Ya kara da cewa lamarin ba wai batun tsaro ba ne kawai, har ma yana dakile mafarkin ‘yan Amurka da ke son samun ilimi a manyan jami’o’i.

'Yan Najeriya na buya a Amurka bayan dokar Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ‘yan Najeriya sun daina fitowa waje saboda fargabar kama su da kuma korarsu daga Amurka, sakamakon tsauraran matakan Donald Trump

Rahotanni sun nuna cewa akalla ‘yan Najeriya 3,690 ne ke fuskantar barazanar kora daga Amurka bisa zargin zama ba bisa ka’ida ba.

Wasu daga cikin su sun bayyana cewa, duk da halin da suke ciki, sun gwammace zaman Amurka a kan komawa Najeriya, wacce ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel