EU Ta Tsoma Baki, Ana So Najeriya Ta Saki Mawakin Kano da Yayi Batanci ga Annabi
- Majalisar Tarayyar Turai ta bukaci Najeriya ta saki Yahaya Sharif-Aminu, mawakin Kano da aka yankewa hukuncin kisa kan batanci
- Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar sakin Sharif-Aminu, amma har yanzu yana tsare yayin da ake jiran hukuncin kotun koli
- Majalisar EU ta bukaci Najeriya ta hana aiwatar da hukuncin kisa, tare da janye dukkanin dokokinta na hukunta laifuffukan batanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Faransa - Majalisar Turai ta nemi hukumomin Najeriya su gaggauta sakin Yahaya Sharif-Aminu, mawakin da aka yanke wa hukuncin kisa a Kano kan batanci.
Majalisar ta bukaci Najeriya ta soke dokokin batanci da suka saba wa kundin tsarin mulkin kasar da alkawuran kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.

Asali: Twitter
Kungiar EU ta nemi Najeriya ta saki Sharif-Aminu
Kola Alapinni, lauya kuma mai kare hakkin dan adam, ya wallafa a shafinsa na X cewa majalisar ta amince da kudurin kiran ba tare da ja-in-ja ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta nuna damuwa kan take hakkin bil’adama a shari’o’in batanci da ake yi a Najeriya, mai neman a mutunta ambaton yarjejeniyoyin kasa da kasa da kundin tsarin mulki.
Kudurin da majalisar EU ta amince da shi ya ce akwai bukatar Najeriya ta mutunta dokar ’yancin addini da fadin albarkacin baki.
Majalisar ta bukaci a saki Sharif-Aminu da sauran wadanda ake tuhuma da batanci ba tare da sharadi ba.
EU ta jinjinawa Najeriya kan sakin Mubarak
Hakanan, an nemi a kyautata yanayin da ake tsare da Sharif-Aminu, tare da ba shi damar samun lafiyayyen abinci, tufafi, da magani.
Majalisar ta jaddada bukatar aiwatar da tsarin daukaka kara a gaban Kotun Koli cikin adalci da gaggawa.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su
Ta kuma yi kira ga Najeriya da ta dakatar da aiwatar da hukuncin kisa a duk fadin kasar.
Har ila yau, Majalisar Turai ta yaba wa Najeriya kan wanke Rhoda Jatau da sakin Mubarak Bala, wadanda aka kama bisa zargin batanci.
Asalin shari’ar Yahaya Sharif-Aminu
A watan Agustan 2020, kotun shari’a ta Kano ta yanke wa Sharif-Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zargin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a cikin wata waka.
Amma a watan Janairun 2021, babbar kotun jihar Kano ta soke hukuncin bisa dalilin kura-kurai a tsarin shari’ar kotun shari’a, tare da bada umarnin sake shari’a.
A watan Agusta 2022, kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin babbar kotun Kano, tana mai soke hukuncin farko kuma ta bada umarnin a sake shari’a.
Yahaya Sharif-Aminu ya garzaya kotun koli
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Yahaya Sharif-Aminu ya garzaya Kotun Koli inda ya kalubalanci hukuncin kisa da kotun shari'ar Kano ta yanke masa.
Ta bakin lauyansa, Kola Alapinni, mawakin wanda aka yankewa hukuncin kisa kan zargin batanci ga Annabi, ya roki Kotun Koli ta ayyana batanci a matsayin ba laifi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng