Batanci ga Annabi: Kotu ta hana Yahaya Sharif-Aminu daukaka kara

Batanci ga Annabi: Kotu ta hana Yahaya Sharif-Aminu daukaka kara

- Yayin da ake kokarin daukaka kara kan hukuncin da aka yankewa mawakin nan da yayi batanci ga Annabi

- Kotun shari'a ta jihar Kano taki bayar da takardun da ya kamata a daukaka karar da su

Kokari na daukaka kara akan hukuncin kisan da aka yankewa mawaki, Yahaya Sharif-Aminu ya kara samun cikas a ranar Talata, bayan shugabannin kotun Shari'a ta jihar Kano sunki bayar da takardun shari'ar na gaskiya.

Sharif-Aminu wanda aka yankewa hukuncin kisa a ranar 10 ga watan Agusta, 2020, bisa laifin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW), an bashi kwanaki 30 ya daukaka kara akan wannan hukunci da aka yanke masa, hakan na nufin ranar Laraba 9 ga watan Satumbar nan ranekun zasu kare.

Batanci ga Annabi: Kotu ta hana Yahaya Sharif-Aminu daukaka kara
Batanci ga Annabi: Kotu ta hana Yahaya Sharif-Aminu daukaka kara
Source: Facebook

Kafin a amince a karbi korafin shi, ana bukatar mai lafin ya sanya hannu akan takardar daukaka karar, inda kuma za a sanya ainahin takardun hukuncin da aka yanke masa a ciki.

Sai dai jaridar PUNCH ta gano cewa an hana Sharif-Aminu ganin lauyansa, yayin da kuma kotun Shari'ar ta ki bayar da takardun hukuncin da aka yanke masa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin PUNCH a ranar Talata, Lauyan dake rajin kare hakkin dan adam Mr Femi Falana (SAN), ya ce yana kokari wajen ganin an gabatar da shari'ar.

Ya ce akwai bukatar a gabatar da komai cikin gaggawa, tunda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a makon da ya gabata yace zai sanya hannu akan hukuncin kisan da aka yankewa mawakin da zarar lokacin da aka diba masa na daukaka kara ya cika.

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin Sakai, sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke

"Sun ki sakin takardun hukuncin da aka yanke masa, kuma lokaci na wucewa. Idan har bamu samu takardun ba baza mu iya daukaka kara ba. Kullum cewa suke takardun basu kammalu ba, kuma lokaci kara kurewa yake," cewar Falana.

Mawakin wanda yake zaune a unguwar Sharifai a jihar Kano, an kama shi da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), a wata waka da yayi da ta dinga yawo a shafukan sadarwa a watan Maris na wannan shekarar.

Matasa dai sun kone gidansu baki daya, kuma sun gabatar da zanga-zanga ga 'yan sanda da hukumar Hisbah akan a gabatar da hukunci akan saurayin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel