Batanci: Sharif-Aminu ya aikata babban laifi da ya cancanci kisa – inji Sheikh Maraya

Batanci: Sharif-Aminu ya aikata babban laifi da ya cancanci kisa – inji Sheikh Maraya

Shararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Haliru Abdullahi Maraya, ya tofa albarkacin bakinsa game da matashin da aka yankewa hukuncin kisan kai.

Haliru Abdullahi Maraya ya bayyana cewa lallai yi wa Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW batanci zai jawowa mutum hukuncin kisa a shari’ar addinin musulunci.

Sheikh Haliru Abdullahi Maraya tsohon mai ba gwamnatin Kaduna shawara ne kan harkokin addini da aikin hajji, kuma babban malami ne wanda ake ji da shi a kasar nan.

Da ya ke magana da jaridar Vanguard, Haliru Abdullahi Maraya a ranar Alhamis, ya goyi bayan hukuncin da babban kotun shari’a ta yankewa Yahaya Sharif-Aminu.

“Game da hukuncin kisa da babban kotun shari’a ta jihar Kano ta yanke a kan wani mawaki da ya zagi Manzon Allah SAW, ina so in ce wannan babban laifi ne kuma ya na jawowa mutum hukuncin kisa.” Inji Shehi.

Maraya ya kara da: “Wannan shi ne matsayar addinin musulunci."

KU KARANTA: Shekau ya soki kisan-kai da sauran abin mamaki da su ka faru a bana

Batanci: Sharif-Aminu ya aikata babban laifi da ya cancanci kisa – inji Sheikh Maraya
Halliru Abdullahi Maraya Hoto: Facebook
Asali: UGC

"Idan ana maganar addinin musulunci, Alkalai su na da hurumin da za su yanke duk hukuncin da ya kamata a doka ga wanda ya yi wa Annabin Allah batanci.”

Sheikh Maraya ya ce: “Wanda aka yankewa hukuncin zai iya daukaka kara idan ya ga dama.”

Shehin ya yi kira ga hukuma da malaman addini su yi kokari wajen wayar da kan al’umma game da martabar fiyayyen halitta da hukuncin wanda ya ci masa mutunci.

Shahararren malamin ya ke cewa idan har aka yi wannan, zai zama an kare darajar Annabi Muhammad SAW daga cin mutuncin masu batanci.

Ina so in yi amfani da wannan dama in yi kira ga jama’a su zauna lafiya da juna. Daukar doka a hannu ba daidai ba ne, mutane su rika aiki da abin da doka ta ce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel