Saudiyya, China da Rasha Sun Ja Kunnen Trump kan Neman Kwace Gaza
- Saudiyya ta bayyana kin amincewa da shirin Shugaban Amurka Donald Trump na mamaye Gaza da tilasta fitar da Falasɗinawa daga ƙasarsu
- Shirin Trump na ƙwace Gaza da tilasta wa 'yan Falasɗinu komawa ƙasashen makwabta ya jawo suka daga ƙasashe da dama a fadin duniya
- Ƙasashe irinsu China, Rasha da ƙungiyoyi na Musulunci a Amurka sun yi Allah-wadai da shirin, suna kira da a mutunta haƙƙin 'yan Falasɗinu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia – Gwamnatin Saudiyya ta bayyana kin amincewarta da wani shiri da shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya bayyana a game da Gaza.
Idan shirin ya tabbata, Amurka za ta mamaye yankin Gaza da tilasta wa 'yan Falasɗinu barin ƙasarsu zuwa ƙasashen makwabta da sunan zaman lafiya.

Asali: Facebook
Legit ta gano martanin da kasar Saudiyya ta yi ne a cikin wani sako da shafin kasar mai suna Inside the Haramaini ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin Donald Trump na kwace Gaza
Trump ya bayyana shirin mamaye Gaza ne a lokacin wani taro tare da Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a Fadar White House.
A cewar Trump, shirin zai sauya fasalin Gaza zuwa wani wuri na daban, inda ya bayyana cewa mutanen duniya za su zauna a can
Furucin ya haifar da babban martani daga ƙasashen duniya, musamman Saudiyya da ke taka muhimmiyar rawa a siyasar Gabas ta Tsakiya.
Martanin Saudiyya ga Trump kan Gaza
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana cewa ba za ta yarda da shirin Trump a Gaza ba, tare da jaddada cewa ba za ta taɓa alakar diflomasiyya da Isra’ila ba sai an kafa ƙasar Falasɗinu.
"Matsayar Saudiyya a bayyane take kuma ba za ta taɓa canzawa ba.
"Mun ƙi duk wani yunkuri da nufin tilasta wa 'yan Falasɗinu barin ƙasarsu ko kuma ƙwace musu haƙƙinsu na mallakar ƙasarsu,"
- Kasar Saudiyya
Saudiyya ta ƙara da cewa tana jaddada ƙin amincewarta da manufofin mamaye ƙasar Falasɗinu da manufofin faɗaɗa yankunan mamaya da Isra’ila ke yi.
Sanatoci sun soki matakin Trump a Gaza
Baya ga Saudiyya, ƙasashen duniya da dama da ƙungiyoyi masu kare haƙƙin dan Adam sun nuna damuwa da adawa da wannan shiri.
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa Sanata Chris Murphy daga Amurka ya bayyana cewa:
“Bai yi tunani mai kyau ba. Mamayar Gaza da sojojin Amurka za su yi zai haifar da mutuwar dubban sojoji da kuma jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin yaƙi na shekaru da dama.”
Shi ma Sanata Chris Van Hollen ya bayyana cewa:
“Shirin Trump na tilasta wa mutane miliyan biyu barin Gaza da mamaye yankin da karfi, wata hanya ce ta kisan kare dangi ta bayan fage.”
China da Rasha sun soki matakin Trump
Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Amurka (CAIR) ta bayyana cewa Gaza mallakin 'yan Falasɗinu ce, ba na Amurka ba.
"Matakin Trump na korar 'yan Falasɗinu daga ƙasarsu ba abin da za a iya kyalewa ba ne.
"Idan wannan zalunci ya faru, zai haifar da rikice-rikice a duniya baki ɗaya kuma ya zubar da martabar Amurka a idon duniya,"
- CAIR
Ƙasar China ta bayyana damuwarta, tana mai cewa tana adawa da duk wani yunkuri na tilasta wa mutane barin ƙasarsu.
“Muna fatan dukkan ɓangarorin za su yi amfani da wannan dama don kawo zaman lafiya da mafita ta siyasa."
- Kasar China
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya bayyana cewa:
“Akwai shirin Isra’ila na neman cikakken iko a yankin Yammacin Kogin Jordan da ƙoƙarin tilasta wa 'yan Falasɗinu barin Gaza.
"Irin wannan tsarin cutar da al’umma baki ɗaya hanya ce da Rasha ke ƙi.”
Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Amurka
A wani rahoton kun ji cewa 'yan Najeriya mazauna Amurka sun fara shiga fargaba yayin da Donald Trump ya tsananta korar bakin haure.
Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa matakin gwamnatin Trump ya sanya su daina zuwa wuraren aiki da ibada domin jin tsoron kama su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng