Kiyama Ta Kusa: Agogon da Ke Hasashen Tashin Duniya Ya Sake Matsawa da Daƙiƙa 1

Kiyama Ta Kusa: Agogon da Ke Hasashen Tashin Duniya Ya Sake Matsawa da Daƙiƙa 1

  • Agogon da ke hasashen tashin duniya ya matsa da dakika daya, wanda hakan ke nufin cewa nan da dakiku 89 za ayi tashin alkiyama
  • Kungiyar BAS ta ce yakin Ukraine da rikicin Gabas ta Tsakiya na iya haddasa mummunan yaki, yayin da ake kara amfani da nukiliya
  • BAS ta jaddada cewa Amurka, China da Rasha suna da karfin ruguza duniyar, don haka su ne ke da alhakin dakile masifar da ke tunkarota

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Chicago - Agogon da aka saita domin ya hasasho lokacin da duniya za ta tashi ya matsa da dakika daya, wanda yanzu ya rage saura dakiku 89 za a yi tashin alkiyama.

Agogon mai suna 'Doomsday Clock' ya sake matsayawa da dakika daya, wanda ya zama mafi kusa da tashin duniya da ya taba kaiwa.

Kara karanta wannan

"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'

Kungiyar BAS ta yi magana da agogon hasashen tashin duniya ya matsa da dakika daya
Agogon da ke hasashen tashin duniya ya matsa da dakika daya a cikin 2025. Hoto: SAUL LOEB / Contributor
Source: Getty Images

Agogon da ke hasashen tashin duniya ya matsa

Ƙungiyar masu nazari kan harkokin kimiyya ta Bulletin of Atomic Scientist (BAS) - wadda ke saita agogon duk shekara, ta yi bayani, a cewar rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar BAS ta sanar da cewa barazanar amfani da makaman nukiliya, yin amfani da fasahohin zamani ta hanyar ba ta dace ba da amfani da AI, hadi da sauyin yanayi, suka jawo matsawar agogon.

Daniel Holz, shugaban mahukuntan kungiyar BAS, ya ce matsawar agogon da dakika daya, "gargadi ne ga shugabannin duniya."

Rahoto ya nuna cewa an fara sanya wa'adin lokacin zuwa ga mintuna bakwai kafin tashin duniya a 1947. A shekarar da ta gabata, ya rage saura dakiku 90 a busa kaho.

"Duniya na daf da halaka" - BAS

A sanarwar BAS (wata kungiya mai zaman kanta da ke a Chicago) ta ranar Talata, kungiyar ta ce:

"Ta hanyar saita agogon zuwa dakika daya ga tashin duniya, wani babban sako ne muke aikawa al'ummar duniya.

Kara karanta wannan

'An sace kudin': Akanta Janar ya tono badakalar biliyoyin Naira a gwamnatin Buhari

"Duniya na daf da fadawa halaka, don haka kowane jinkiri wajen daukar mataki yana kara kusanto da afkuwar bala’in ne."

Kungiyar ta yi gargadin cewa yakin da ake yi a Ukraine da ya kusan cika shekaru uku yana iya rikidewa zuwa yakin nukiliya a kowanne lokaci.

Sanarwar ta kuma nuna damuwa cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya rikidewa zuwa babban yaki ba tare da mutane sun farga ba.

BAS ta gargadi kasashen China, Amurka da Rasha

Masana kan kimiyyar sun kuma bayyana cewa gwamnatoci ba su dauki matakan rage dumamar yanayi yadda ya kamata ba.

Kungiyar BAS ta kuma yi gargadi cewa ci gaban fasahar zamani da aka samu a shekarar da ta gabata yana kara zama hadari ga duniya.

Ana amfani da tsarin AI a yakin Ukraine da Gabas ta Tsakiya, kuma wasu kasashe na kokarin shigar da fasahar a harkar soja.

BAS ta jaddada cewa Amurka, China da Rasha suna da karfin ikon hallaka duniya, don haka su ne ke da alhakin dakatar da barazanar.

Kara karanta wannan

Bauchi: Ana zargin kwamishina da sace yarinya, wanda ake tuhuma ya fayyace lamarin

Masana kimiyya sun hango tashin duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masana kimiyyar sararin samaniya sun ci karo da wasu takardu da ke bayani game da lokacin tashin duniya da Isaac Newton ya rubuta.

Takardun da Newton ya rubuta a karni na 16 bayan haihuwar Annabi Isa AS sun nuna cewa a 2060 ne Annabi Isa zai dawo duniya, kuma akwai yiwuwar duniya ta tashi a shekarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com