'Ba Daga Dabbobi ba ne': Amurka Ta Fadi Sunan Kasar da Ake Zargin Ta Kirkiro Covid19

'Ba Daga Dabbobi ba ne': Amurka Ta Fadi Sunan Kasar da Ake Zargin Ta Kirkiro Covid19

  • Hukumar CIA ta ce akwai yiwuwar COVID-19 ta fito ne daga dakin gwaje-gwaje a China, amma ba ta da tabbas kan hasashen
  • CIA ta fitar da wannan rahoton ne jim kadan bayan da aka rantsar da Shugaba Donald Trump, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce
  • Yayin da WHO ta ce Corona ta samo asali daga beraye, kasar China ta fito ta karyata zarge-zargen Amurka na samuwar cutar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Hukumar CIA ta ce annobar COVID-19 ta fi kama da ta barke ne daga wani dakin gwaje-gwaje a China sabanin ace daga dabbobi ta fito.

Wannan sabon rahoton ya fito ne bayan wani bincike da aka fara karkashin mulkin Biden, bisa umarnin tsohon daraktan CIA, William Burns.

CIA ta yi bayani da ta fitar da rahoto kan assalin cutar Covid-19
CIA ta yi ikirarin cewa COVID-19 ta samo asali ne daga wani dakin gwaje-gwajen China. Hoto: Yuichiro Chino, Tom Williams
Asali: Getty Images

CIA ta hasasho inda Covid-19 ta fito

Shekaru da dama CIA tana cewa ba a tabbatar ko COVID-19 ta fito daga dakin gwaje-gwaje ko daga dabbobi ba, sai ga shi kwatsam ta fitar da wannan rahoton, inji Sky News.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sabon rahotonta, hukumar CIA ta nuna cewa China ce ke da alhakin fitar da cutar, ko da yake ta ce tana da "ƙarancin tabbaci" game da wannan karshe.

Rahoton CIA bai dogara da wata sabuwar hujja ba, sai dai sababbin nazari kan bayanan yadda annobar ta yadu da halayen kimiyyar cutar.

Ra'ayin Ratcliffe kan bullar annobar Covid-19

Har yanzu CIA ta dage kan cewa annobar Covid-19 ta barke ne a dayan biyu: ko dai daga dakin gwaje-gwaje ko ta dabi’a.

An fitar da rahoton ne ranar Asabar bisa umarnin John Ratcliffe, wanda Shugaba Trump ya naɗa a matsayin shugaban leƙen asiri na Amurka.

John Ratcliffe ya ce daya daga cikin ayyukansa na farko shi ne tabbatar da fitar da wannan nazari kan asalin cutar Covid-19 ga jama’a.

A hirarsa da Breitbart News, ya ce tun farko ya nuna ra’ayin cewa COVID-19 ta fito daga dakin gwaje-gwaje a Wuhan.

Kara karanta wannan

Wata tankar man fetur ta sake fashewa a jihar Neja, ana fargabar mutane sun mutu

WHO ta yi tsokaci kan ikirarin Amurka

Rahotanni na baya sun rarrabu kan ko annobar ta samo asali daga wani bincike na China ko kuma daga Ubangiji ce.

A watan Maris 2021, wani rahoto daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce COVID-19 ta fi kama da wacce ta fito daga beraye.

Rahoton WHO ya ce akwai shakku sosai a ikirarin cutar ta fita daga dakin gwaje-gwaje a Wuhan, amma ya ce ba za a iya janye zargin kwata kwata ba.

Har ila yau, rahoton ya musanta ra’ayin cewa an ƙera ko kuma an fitar da cutar daga dakin gwaje-gwaje da gangan.

China ta karyata ikirarin Amurka

A watan Mayu 2023, wani babban masanin kimiyya daga China ya ce ba za a cire yiwuwar COVID-19 ta fita daga dakin gwaje-gwaje ba.

Gwamnatin China ta ce tana goyon bayan gudanar da bincike kan asalin Corona, amma ta zargi Amurka da siyasantar da al’amarin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Beijing ta ce zarge-zargen da ke cewa barkewar annobar ta samo asali daga dakin gwaje-gwajen Wuhang ba su da tushe, inji rahoton Reuters.

A cewar CIA, za ta ci gaba da nazarin sababbin bayanai da za su iya sauya matsayinta a nan gaba.

Duk da haka, rahoton ya nuna akwai bukatar karin bincike da cikakken bayani don tabbatar da asalin COVID-19.

Mutane na iya hadawa mage cutar corona

A wani labarin, mun ruwaito cewa binciken da masana kimiyya daga kasar Italiya suka gudanar ya nuna cewa mutane na iya yada cutar korona ga kuliyoyi da karnuka.

A lokacin binciken, an gwada karnuka 540 da kuliyoyi 277 da ake kiwo a gidaje a Arewacin Italiya, musamman a lardin Lombardy, inda cutar korona ta fi yaduwa tsakanin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel