Mutane na iya yada wa kuliyoyi da karnuka cutar korona

Mutane na iya yada wa kuliyoyi da karnuka cutar korona

Binciken da masanan kimiyya na kasar Italiya suka gudanar ya gano cewa mutane na iya yada cutar korona zuwa ga kuliyoyi da karnuka.

Yayin binciken, an gwada karnuka 540 da kuliyoyi 277 da ake kiwonsu a cikin gidaje a Arewacin Italiya, musamman lardin Lombardy, inda cutar korona tafi kamari a tsakanin mutane.

Binciken wanda bai samu bitar sa'anni ba a fannin ilimi, sai dai an gano cewa, akwai kashi 3.4 zuwa kashi 3.9 cikin dari na kwayoyin cutar a jikin karnuka da kuliyoyin da aka yi wa gwajin cutar.

Hakan ya tabbatar da cewa karnukan da kuliyoyin sun kamu da cutar Covid-1 yayin binciken da aka gudanar a tsakanin watan Maris da Mayun shekarar.

Hoton kuliya daga jaridar Daily Nigerian
Hoton kuliya daga jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Thomas Mettenleiter, shugaban cibiyar binciken lafiyar dabbobi ta kasar Jamus, ya ce sakamakon ya nuna yadda cutar zata iya yaduwa a tsakanin dabbobi da bil'adama.

Ya kara da cewa, "wannan ya bamu tabbaci kan abin da muka riga muka sani". Yana mai cewa "wannan bincike ba a taɓa yin makamancinsa ba tun da yana da wahala a iya daukan samfuri a jikin dabbobin."

A cewar Mettenleiter, mafi akasarin dabbobin da aka gudanar da bincike a kansu sun kasance dabbobin da ake kiwo a gida, wanda hakan ya kara nuna tabbaci kan yaduwar cutar tsakanin mutane da dabbobi.

KARANTA KUMA: WAEC: Za a buɗe duk makarantun tarayya 104 a ranar Talata - Nwajiuba

Ya kara da cewa, wannan bincike ya tabbatar da cewa kuliyoyi da karnuka basu da wani tasiri wajen yaduwar cutar, saboda haka kada mutane masu lafiya suka rika yin nesa-nesa da su.

Sai dai ya ce mutane masu dauke da kwayoyin cutar, su takaita cuɗanya da dabbobin duk da dai har yanzu babu alamun da ke nuna cewa dabbobin na iya mutuwa sakamakon cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel