Daga Rantsar da Shi, Trump Ya Kori Mace Ta Farko da Ta Shugabanci Sojojin Amurka

Daga Rantsar da Shi, Trump Ya Kori Mace Ta Farko da Ta Shugabanci Sojojin Amurka

  • Donald Trump ya kori shugabar sojojin ruwa, Adm. Linda Fagan, cikin sa’o’i 24 bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa
  • An ce Amiral Fagan ta kasa magance barazanar tsaro a iyakoki, musamman shigo da miyagun kwayoyi da matsalolin cin zarafi
  • Sai dai kuma, wasu bayanai da suka bayyana sun ce akwai wata makarkashiya a sauke Admiral Fagan daga wannan mukamin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - An kori shugabar sojojin ruwan Amurka, Adm. Linda L. Fagan, cikin sa’o’i 24 bayan rantsar da Shugaban Kasa Donald Trump.

Admiral Fagan ta kasance mace ta farko da ta jagoranci wata rundunar sojojin Amurka, kuma an nada ta ranar 1 ga watan Yunin 2022.

Gwamnatin Trump ta yi bayani da aka tsige shugabar sojojin ruwan Amurka, Admiral Fagan
Trump ya sauke shugabar sojojin ruwan Amurka kasa da sa'o'i 24 da rantsar da shi. Hoto: @realDonaldTrump, @JEHutton
Asali: Twitter

Donald Trump ya kori shugabar sojojin Amurka

Sakataren tsaron cikin gida, Benjamine Huffman, ya aika sakon sauke Admiral Fagan ga dukkanin sassan sojojin ruwan a ranar Talata, inji rahoton New York Times.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ta taka rawar gani a tsawon lokacin aikinta, ina yi mata godiya bisa hidimar da ta yi wa al'ummarmu," in ji Mista Huffman.

Sai dai sakataren tsaron bai bayyana dalilin da ya sa aka gajarta wa'adin aikin Admiral Fagan a cikin sanarwar ba.

Wasu dalilai na korar shugabar sojojin ruwan

Amma kuma wata sanarwa mai tsawo daga ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka ta bayyana cewa an kori Fagan ne saboda matsaloli da suka shafi manufofin Trump.

Sanarwar ta ce an sallame ta saboda rashin iya jagoranci, gazawar aiki da kuma kasa cimma manyan burikan sojojin ruwan.

Ana zargin cewa Admiral Fagan ta kasa magance barazanar tsaro a iyaka, musamman hana shigo da miyagun kwayoyi kamar fentanyl.

An kuma soki salon jagorancinta wajen daukar ma’aikata, kiyaye su da kuma kula da sayen na’urorin aiki kamar jirage masu saukar ungulu da na’urar yankan kankara.

An maye gurbin Admiral Fagan da mataimakinta

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki

Sanarwar ta ce ta fi mayar da hankali kan manufofin bambance-bambance, daidai wa daida, da kuma shigar da kowa cikin tsare-tsare, inji rahoton Aljazeera.

An zarge ta da kasa magance matsalolin cin zarafin jima’i da suka shafi jami’an makarantar horar da sojojin ruwa da ke New London, Connecticut.

An kasa samun Admiral Fagan don ta yi sharhi kan batun tun ranar Talata, haka kuma mai magana da yawun sojojin ruwan ya ki yin karin bayani.

Sanarwar ta ce Adm. Kevin E. Lunday, wanda shi ne mataimakin Fagan, yanzu shi ne mukaddashin shugaban sojojin ruwan.

Trump ya jinjinawa dansa, Barron

A wani labarin, mun ruwaito cewa an rantsar da shugaban kasar Amurka na 47, Donald Trump a ranar Litinin domin jagorantar kasar a karo na biyu.

A wajen bikin rantsar da shi, Donald Trump ya gabatar da dansa, Barron ga mahalarta taron inda ya jinjina masa da cewa ya taimaka wajen nasararsa a 2024.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi yadda aka zuba jarin $6.7bn a bangaren makamashi

Mun zakulo wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Barron Trump ciki har da tsayinsa mai ban mamaki yana mai shekara 18 a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.