Amurka: Fada Ya Barke Tsakanin Shugaban Kasa da Gwamna da Gobara Ta Kashe Mutum 24

Amurka: Fada Ya Barke Tsakanin Shugaban Kasa da Gwamna da Gobara Ta Kashe Mutum 24

  • Donald Trump ya tsananta suka kan yadda ake tafiyar da gobarar California, inda ya ce: "Ba su iya kashe gobarar ba, me ke damunsu?"
  • Da yake martani, gwamnan California ya bukaci Trump ya zo ya ga irin barnar da gobarar ta yi da kansa ba wai magana daga nesa ba
  • Sai dai Trump ya yi barazanar katse tallafi ga California, lamarin da gwamnan ya ce bai kamata a siyasantar da batun iftila'in ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya tsananta suka ga yadda California ke tafiyar da gobarar da ke addabar Los Angeles.

Sai dai gwamnan jihar California, Gavin Newsom ya bukaci Trump ya daina magana daga nesa, ya zo ya ga irin karfi da barnar da gobarar ta yi da kansa.

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

Ana ta cacar baki tsakanin Donald Trump da gwamnan California kan gobarar Los Angeles
Donald Trump ya zargi shugabannin California da sakaci a kashe gobarar da ta kashe mutum 24. Hoto: ANGELA WEISS/AFP
Asali: Getty Images

Trump ya soki shugabanni kan gobarar Amurka

Rahoton mujallar Forbes ya nuna cewa adadin mutanen da suka mutu daga wannan gobarar ya karu zuwa 24, ciki har da 16 daga gobarar yankin Eaton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakanan, akwai mutane takwas da suka rasa rayukansu a gobarar Palisades da ke cikin birnin Los Angeles.

Da ya ke tsokaci kan gobarar California a dandalinsa, Trump ya ce:

"Har yanzu gobarar na ci gaba da ruruwa a L.A. 'Yan siyasa da ba su da kwarewa sun rasa hanyar kashe wutar."
"Wannan na daga cikin manyan masifu a tarihin ƙasarmu, amma ba su iya kashe gobarar ba. Me ke damunsu?"

Gwamnan California ya yi wa Trump martani

Gwamna Gavin Newsom, wanda Trump ya dade yana suka, a zantawarsa da kafar labaran NBC ya ce:

"Domin mayar da martani ga cin mutuncin Donald Trump, za mu iya kwashe wata guda. Duk dan siyasar da ya saba da shi ya saba da irin wadannan kalaman."

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

Duk da haka, Newsom ya ce ya gayyaci Trump ya je California ya ga halin da suke ciki da kansa, ya cire gaba, ya kalli lamarin a fuskar hadin kai da neman mafita.

Gwamnan ya kara da cewa har yanzu bai samu amsa daga Trump kan wannan gayyatar ba.

An yi musayar yawu tsakanin Trump da gwamna

To sai dai kuma an ce Trump ya kira Newsom da sunan ba’a, "Newscum," lamarin da ya sa gwamnan ya ce dole ne a kauce wa siyasantar da wannan iftila'in.

Newsom ya rubuta wa Trump wasika cewa: "Na gayyace ka zuwa California ka ga barnar da gobarar ta yi da idonka, amma har yanzu na jika shiru."

An ce Trump ya yi barazanar yanke tallafin kashe gobara ga California, amma Newsom ya jaddada cewa bai kamata zababben shugaban ya siyasantar da annobar ba.

Trump ya yi wa Najeriya barazana kan Kanu?

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani bidiyo na bogi ya bayyana, inda aka nuna zababben shugaban Amurka, Donald Trump, yana kiran Najeriya ta saki Nnamdi Kanu.

An ce Trump ya bai wa Najeriya wa’adin 31 ga Nuwamba ta saki Nnamdi Kanu ko ta fuskanci fushinsa, amma wannan ba gaskiya ba ne.

Bidiyon TikTok din da aka ruwaito an tsara shi ta hanyar fasahar AI daga jawabin Trump na nasara bayan lashe zaɓe a Nuwamba 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.