A karon farko an samu Alkali Musulmi a birnin California na kasar Amurka

A karon farko an samu Alkali Musulmi a birnin California na kasar Amurka

- Birnin California na kasar Amurka gari ne da ba a taba samun alkali Musulmi ba sai a wannan karon

- Alkalin wanda yake dan asalin kasar Indiya sun koma yankin gabashin Afrika da zama tare da iyayenshi kafin nan suka wuce kasar Amurka

- Mutane sun yi shedar alkalin akan halaye na kirki da kuma gabatar da shari'a kan adalci

Birnin California ya bar babban tarihi, yayinda suka samu babban alkali Musulmai na farko, duk kuwa irin nuna kyamar Musulunci da ake yi a yankin Arewacin Amurka. Rahoton PBS.

Alkalin Musulmi dan kasar Amurka, Halim Dhanidina an bashi wannan mukami a kotun daukaka kara, hakan ya sanya ya zama alkali Musulmi da yafi kowa karfin iko a yankin.

A karon farko an samu Alkali Musulmi a birnin California na kasar Amurka
A karon farko an samu Alkali Musulmi a birnin California na kasar Amurka
Asali: Facebook

“Na koyi hakuri da maganganun mutane na cin mutunci, shin mai kuke tunanin zai faru inda ace babu wani alkali Musulmi. Zanyi kokari wajen ganin na bar misali ga kowa da kowa,” in ji shi.

Mutane da yawa masu kyamar Musulunci da kuma masu kyamar baki, sun ta nuna rashin goyon bayansu akan mukamin da Dhanidina ya samu, inda suke tambayar wacce gudummawa zai bayar a fanin damokuradiyya.

KU KARANTA: Mutumin kasar Netherlands da ya fi kowa tsanar Musulunci a duniya ya Musulunta

Dhanidina an haifeshi a yankin Gujarati na kasar Indiya, inda iyayenshi suka yi hijira zuwa yankin gabashin Afrika kafin daga nan suka koma kasar Amurka. A matsayinshi na uba, Dhanidina yana shafe yawancin lokacin shi tare da ‘ya’yanshi. Amma a ranekun aiki, yana aiki tukuru wajen ganin yayi hukuncin da ya dace da kowacce shari’a da ta zo gabansa.

Wata ta hannun damar Dhanidina, Rachel Andres, wacce take Bayahudiya ce ta ce: “Ya damu sosai da al’umma, Musulmai, Yahudawa, Kiristoci, alakar mutane, adalci, da dai sauransu.”

“Na sanshi sama da shekaru hudu da suka wuce, a lokacin naji ya zame mini kamar wata katangar dafawa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng