Ghana: Bidiyon Yadda Dogarin Shugaban Kasa Ya Kife a cikin Majalisa, An Kai Shi Asibiti

Ghana: Bidiyon Yadda Dogarin Shugaban Kasa Ya Kife a cikin Majalisa, An Kai Shi Asibiti

  • A yau Juma’a, 3 ga Janairu 2025, Kanal Isaac Amponsah, mai tsaron lafiyar Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana ya fadi a cikin majalisa
  • Mai girma Shugaba Akufo-Addo ya dakatar da jawabin nasa na ƙarshe don tabbatar da cewa an kula da lafiyar mai tsaronsa
  • Likitocin majalisa sun yi gaggawar bada agaji ga Kanal Amponsah, sannan aka garzaya da shi asibiti don duba lafiyarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Accra, Ghana - Wani abin tausayi ya faru yayin da shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ke jawabi a Majalisa.

Lamarin ya faru ne a cikin majalisa a ranar Juma’a, 3 ga Janairu 2025, yayin da dogarin Akufo-Addo, Kanal Isaac Amponsah ya fadi a lokacin jawabin shugaban ƙasa.

Dogarin shugaban kasa ya fadi a cikin Majalisa
An yada bidiyon yadda dogarin shugaban kasar Ghana ya fadi kasa a cikin Majalisa. Hoto: Joy News.
Asali: Youtube

Dogarin shugaban kasa ya fadi a Majalisa

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa na YouTube, jami'an lafiya sun yi gaggawar kawo dauki ga dogarin shugaban.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kaɗan bayan da Shugaba Akufo-Addo ya fara jawabin nasa, Kanal Amponsah ya yi kasala ya fadi ba tare da wata alamar gargadi ba.

Bidiyon ya nuna yadda likitocin majalisa suka yi gaggawar zuwa wurin don ba shi taimakon gaggawa.

Bayan an ba shi kulawa na farko, sai aka kai shi wani asibitin kusa don bincike da ƙarin kulawa.

Abin da Akufo-Addo ya yi bayan fadin dogarinsa

A yayin da lamarin ya faru, Shugaba Akufo-Addo ya dakatar da jawabinsa na ɗan lokaci don tabbatar da cewa mai tsaronsa ya samu taimakon da ya dace.

Daga baya ya ci gaba da jawabin inda ya bayyana ci gaban da aka samu a mulkinsa da kuma makomar Ghana.

A halin yanzu, babu wani bayani kan lafiyar Kanal Amponsah, amma ana sa ran samun karin bayani nan ba da jimawa ba.

Wannan lamari ya sanya yanayin tausayawa a cikin wannan rana mai muhimmanci ta shugabancin Akufo-Addo.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Ghana ta yi yunkurin taimakawa Najeriya da wuta

Kun ji cewa Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Ghana ta yi alkawarin taimakawa Najeriya da wutar lantarki.

Kasar ta ce za ta taimakawa Najeriya wurin tabbatar da samun kaso 100 na karfin wutar lantarki a duniya.

Shugaban hukumar, Henson Monney shi ya bayyana haka a jihar Legas yayin taron makamashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.