Yanzu-yanzu: Nana Akufo-Addo ya lashe zaben kasar Ghana
- Bayan kwanaki ana fafatawa a bakin akwati, an sanar da wanda yayi nasara
- An sanar da sakamakon duk da cewa ba'a kammala hada kuri'un yanki guda ba
- Baturiyar zaben alanta wanda yayi nasara matsayin zababben shugaba
Shugaba Nana Akufo-Addo ya lashe zaben shugaban kasan Ghana, inda ya lallasa abokin hamayyarsa kuma tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama.
Akufo-Addo ya samu nasara da kuri'u 6,730,413 (51.59%) yayinda mai biye da shi Dramani Mahama ya samu kuri'u6,240,889 (47.36%).
Mr Akufo-Addo, wanda yayi takara karkashin jam'iyyar New Patriotic Party NPP, ya lashe kuri'un yankuna 8 cikin 16 yayinda Mahama ya lashe 8.
Shugabar hukumar zaben Ghana, Jean Mensah, ta ce an sanar da sakamakon ne ba tare da yankin Techiman ta kudu saboda ana ja-in-ja kai.
Ta ce amma tunda gaba daya kuri'un yankin 128,018 ne, ba zai canza sakamakon zaben ba.
"Bisa ikon da aka bani a matsayin baturiyar zabe, hakki na ne in sanar da Nana Akufo-Addo a matsayin zababben shugaban kasar Ghana," tace.
KU KARANTA: Alkalin Kotun koli ya tabbatar da nasarar Joe Biden a Jihar Pennsylvania
KU KARANTA: 2020: Fitattu 8 a Najeriya da suka siya wa iyayensu motoci da gidaje
A bangare guda, annobar korona ta haifar da dubban mace-mace a fadin duniya sannan ta durkusar da tattalin arzikin duniya.
A yayinda shekarar 2020 ke shirin karewa, Legit.ng ta duba wasu manyan yan siyasar da suka mutu a wannan shekara, mafi akasarinsu korona ce ta kashe su.
Karanta jerin mutanen a nan: https://hausa.legit.ng/1391109-kyari-da-manyan-yan-siyasa-9-da-suka-mutu-a-2020-jerin-sunaye.html
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng