EndSARS: Na tattauna da Buhari - Shugaban Ghana, Akufo-Addo
- Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana ya bayyana cewa Shugaba Buhari a shirye ya ke ya yi sulhu da masu zanga-zanga
- Akufo-Addo ya sanar da hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na dandanlin sada zumunta ta Twitter
- Shugaba Akufo-Addo ya yi kira ga masu zanga-zanga da 'yan sanda su guji tashin hankali kana ya mika sakon ta'aziyyarsa da wadanda suka rasu
Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga Shugaba Buhari da yin sulhu da masu zanga-zangar #ENDSARS.
Ya yi gargadin cewa rikici bashi zai kawo karshen matsalar zanga zangar da ake don nuna bacin rai kan muguntar yan sanda.
Akufo-Addo ya ce ya yi magana da Shugaba Buhari kan matsalar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 21 ga watan Oktoba.
DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas
Shugaban na Ghana ya cewa shugaba Buhari a shirye yake don yin sulhu.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter, "Nabi sahun mutane masu kima wajen kira da a zauna lafiya, da kuma amfani da sulhu wajen kawo karshen rikicin #ENDSARS a Najeriya. Nayi magana da shugaba Buhari kuma ya tabbatar min a shirye yake don yin sulhu, kuma tuni shiri yayi nisa don kawo karshen matsalar".
"Tashin hankali, daga bangaren masu zanga-zanga ko 'yan sanda ba zai warware matsalar ba. Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa ;yan uwansu sannan ina yi wa wadanda suka samu rauni fatan samun sauki cikin gaggawa."
KU KARANTA: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi wa masu zanga-zanga jawabi. Ya gargadi cewa kada shugaban yayi amfani da karfin hukuma akan masu zanga-zangar #ENDSARS.
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa daya gabata ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter ranar Talata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng