Jerin Sunaye: Kasashen Afrika 5 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa ba Tare da Biza ba

Jerin Sunaye: Kasashen Afrika 5 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa ba Tare da Biza ba

  • Ana ƙara yunƙurin kawar da biza a tafiye-tafiye a Afirka, inda ƙasashe kamar Rwanda da Kenya suka buɗe iyakokinsu
  • Ƙasashe guda biyar na Afirka sun yi zarra wajen ba da damar shiga ƙasashensu ba tare da buƙatar bisa ba daga 'yan Afirka
  • Manufofin waɗannan ƙasashen shi ne ƙarfafa yawon buɗe ido, kasuwanci da haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ana samun ci gaba a yunƙurin ba da damar tafiye-tafiye ba tare da biza ba a Afirka, inda ƙasashe kamar Rwanda da Kenya suka buɗe iyakokinsu ga dukkanin 'yan Afirka.

Wannan yunƙuri na da nufin ƙarfafa haɗin kai, ci gaban tattalin arziki da kuma musayar al'adu a nahiyar Afrika.

Kenya da wasu kasashen Afrika 5 da ake zuwa ba tare da Biza ba
An samu jerin manyan kasashen Afirka d aba sa bukatar Biza daga matafiya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Duk da cewa ba duka kasashen Afrika ne suka amince a shiga cikinsu ba tare da bisa ba, amma rahoton Vanguard ya lissafa kasashe biyar da suka rungumi wannan tsarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace malamin addini, sun bukaci N75m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Seychelles

Seychelles ta kasance jagaba wajen inganta tafiye-tafiye ba tare da biza ba.

Tun shekarar 2018 ta zama ƙasar Afirka daya tilo da ke bayar da damar shiga ba tare da biza ba ga dukkanin 'yan kasashen duniya, ciki har da 'yan Afirka.

Kasar Seychelles ta ci gaba da zama misali kan yadda sassauta takunkumi kan tafiye-tafiye ke ƙarfafa yawon buɗe ido da ci gaban tattalin arziki.

2. Gambia

A shekarar 2019, Gambia ta sanar cewa za ta bai wa dukkan 'yan ƙasashen Afirka damar shiga cikinta ba tare da biza ba.

Haka kuma ta ba da damar ga ƙasashen Commonwealth, ƙasashen Tarayyar Turai (EU), da 'yan ƙasar Belgium masu katin shaida na doka.ow a

Wannan mataki ya ƙarfafa yunƙurin haɗa kan kasashen da sauƙaƙa tafiye-tafiye.

3. Benin

A shekarar 2019, Benin ta jawo hankulan kasashe lokacin da Shugaba Patrice Talon ya cire duk wasu buƙatun biza don shiga ƙasar.

Kara karanta wannan

Jihohin Najeriya sun yi kasafin sama da N74trn don magance talauci a 2025

Yayin da ya yi koyi da irinsu Rwanda, wannan mataki na Benin ya ƙarfafa dangantaka tsakanin yankuna kuma ya sauƙaƙa wa 'yan Afirka ziyartar wannan ƙasa ta Yammacin Afirka.

4. Kenya

A watan Oktoba 2023, shugaban Kenya William Ruto ya bayyana cewa za a soke duk wasu buƙatun biza ga baƙin yawon buɗe ido na Afirka.

An tsara hakan ne don tabbatar da Kenya a matsayin cibiyar kasuwanci da yawon buɗe ido, da haɓaka dangantakar tattalin arziki a nahiyar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

5. Rwanda

Rwanda ta shiga jerin ƙasashen da ba sa buƙatar biza a watan Nuwamba 2023, lokacin da ta sanar cewa dukkanin 'yan Afirka za su iya ziyartarta ba tare da biza ba.

Shugaba Paul Kagame ya jaddada rawar da Rwanda ke takawa a matsayin cibiyar kasuwanci da yawon buɗe ido a Gabashin Afirka, tare da ƙarfafa yunƙurinta na zama kasar matafiya.

Kasashe 44 da ba sa bukatar biza

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsaka da bikin Kirsimeti, sun hallaka bayin Allah

A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa akwai wasu kasashe 44 da 'yan Najeriya masu fasfo din tafiye-tafiye za su iya ziyartarsu ba tare da sun nemi Biza ba.

Najeriya ta koma ta 95 a ƙasashe 104 masu ƙarfin fasfo kamar yadda rahoto ya nuna, wanda ya sa 'yan kasar ke iya shiga wasu kasashe ba tare da Biza ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.