Kasashen Afirka 7 da 'yan Najeriya za su iya ziyarta ba tare da biza ba

Kasashen Afirka 7 da 'yan Najeriya za su iya ziyarta ba tare da biza ba

Duk dan Najeriya da ke son tafiya kasashen ketare yana bukatar shiri duba da cewa fasfo din Najeriya ce ta 83 a duniya hakan na nuna cewa samun biza na zuwa kasahen ketare ba abu na mai sauki ba.

Sai dai duk da hakan akwai kasashen Afirka da 'yan Najeriya za su iya tafiya da fasfo din su ba tare da yin biza ba. Wasu kuma na bukatar mutum ya nemi izinin samun bizan idan ya tafi shiga kasar.

Ga jerin kasashen da 'yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba:

1 - Morroco

Kasar Morroco na da yanayi mai kyau gashi al'ummar kasar na da al'adu masu kyau wanda hakan yasa masu yawon bude ido suke sha'awan zuwa kasar. Akwai wuraren cin abinci na zamani da manyan shaguna don masu siyaya da sauransu.

2 - Sudan

Duk wani dan Najeriya da ke sha'awar zuwa Sudan yana iya tafiya kuma ya samu biza daf da zai shiga kasar. Akwai namun daji masu ban sha'awa a kasar.

DUBA WANNAN: Tsaffin gwamonin APC uku da ake kyautata zaton Buhari zai nada ministoci

3 - Cape Verde

Kasar Cape Verde kasa ce a Afirka ta Yamma wacce ke zagaye da ruwa. Hakan yasa masu yawon bude ido da zuwa hutu suke tururuwa zuwa kasar. 'Yan Najeriya na iya zuwa kasar ba tare da biza ba.

4 - Kenya

Kasar Kenya na da dabobin daji sosai da ke jan hankulan masu yawon bude ido. Manyan biranen da suka fi shahara a kasar sun hada na Nairobi da Mombassa inda galibin mutanen kasar ke maraba da baki. 'Yan Najeriya na iya samun biza yayin shiga kasar.

5 - Uganda

Uganda tana gabashin Afirka ne. Kasar na da nau'ikan abinci kala-kala da kuma wuraren yawon bude ido da suka hada da Tafkin Victoria da sauransu. 'Yan Najeriya na iya samun bisa yayin shiga kasar.

6 - Djibouti

Djibouti kasa ce da ke gabashin Afirka. Tana daya daga cikin kasashen da 'yan Najeriya za su iya kai ziyara cikin sauki kuma mutum yana iya samun biza cikin sauki yayin shiga kasar. Kasar tana da wuraren bude ido masu ban sha'awa kamar Tafkin Assal da sauransu.

7 - Rwanda

Rwanda tana daya daga cikin kasahe mafi tsafta a Afirka kuma ta masu saka hannun jari da yawon bude idanu suna yawan zuwa kasar. Tun bayan yakin basasa da akayi a kasar a 1994, kasar ta yi canje-canja da dama.

'Yan Najeriya suna iya samun biza kan kudi N36,000 a yayin shiga kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164