Suna 'Muhammad' Shi ne Wanda Aka Fi Radawa Jarirai a Burtaniya, Ya Zarta Nuhu

Suna 'Muhammad' Shi ne Wanda Aka Fi Radawa Jarirai a Burtaniya, Ya Zarta Nuhu

  • Sunan Muhammad ya zarce na Nuhu a cikin jerin sunayen da aka fi sakawa jarirai maza a kasar Burtaniya da ke Nahiyar Turai
  • Wani bincike ya tabbatar da cewa an yi rijistar sunayen jarirai 4,600 a shekarar 2023 a kasashen Burtaniya da Wales
  • Sunan Muhammad ya kasance daga cikin jerin sunayen da aka fi sanyawa jarirai tun 2016 kafin ya zarce Nuhu a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

London, Burtaniya - Wani bincike ya tabbatar da yawan sanyawa jarirai suna Muhammad ya karu inda ya zama mafi farin jini.

Rahoton ya ce a Burtaniya da Wales iyaye sun fi sanyawa jariransu Muhammad a shekarar 2023.

Muhammad ya zama suna mafi farin jini a Burtaniya
Hukumar kididdiga a Burtaniya ta ce Muhammad ya fi kowane suna farin jini. Hoto: Getty Images. (An yi amfani da hoton domin misali. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa).
Asali: Getty Images

An yi rijistar sunan Muhammad 4,600 a Burtaniya

Reuters ta ce an yi rijistar sunayen jarirai da sunan Muhammadu guda 4,600 wanda ya zarce Noah (Nuhu) da ya fi yawa a baya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Kotun Jigawa ta yankewa miji da mata da 'yanuwanta 2 hukuncin kisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a shekarar 2016, Muhammad na daga cikin manyan sunaye 10 da ake yawan sakawa amma yanzu ya zarta Noah da aka fi yawan amfani da shi.

Hukumar kididdiga ta Burtaniya (ONS) ta ce a bangaren jarirai mata kuwa sunan Olivia ke kan gaba.

Sunayen mata da suka yi fice a Burtaniya

Bayan Olivia akwai sunaye biyu da ke biye mata da suka hada da Amelia da kuma sunan Isla, cewar The Guardian ta Burtaniya.

Sai dai rahoton ya ce akwai yankunan kasar guda uku da sunan Muhammad bai fito cikin jerin sunaye 10 ba saboda bambance-bambance.

Sababbin sunayen mata da suka shiga jerin wadanda suka fi farin jini guda 100 sun hada da Lila da Raya da kuma Hazel.

An haramta sanya suna Muhammad a Sin

A wani labarin, kun ji cewa a 2017 gwamnatin kasar Sin, ta haramtawa iyaye sanya sunaye irinsu Muhammad a matsayin sunayen jariran.

Kara karanta wannan

'Dan shekaru 100 ya auri mai shekaru 102, sun kafa tarihi a duniya

Sauran sunayen sun hada da ‘Arafat’ da kuma ‘Jihad’ kamar yadda rahotonni su ka bayyana domin a dakusar da duk wani kishin addini a kasar.

Wannan doka ta na aiki ne a yammacin birnin Xinjiang inda ake da tarin Musulmai daga cikin mutanen Uighurs wadanda adadinsu ya haura miliyan 10.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.