Yaki da addini: Babu wanda ya isa ya sa wa yaro suna Muhammad a Sin tun 2017
Mutane da-dama ba su da labarin cewa yaki da addinai musamman musulunci da gwamnati ta ke yi a kasar Sin, ya na kara karfi a yanzu.
A cikin 2017 ne aka ji gwamnatin kasar Sin, ta haramtawa iyaye zaben sunaye irinsu Muhammad a matsayin sunayen yankan jariran da su ka haifa.
Sauran sunayen da aka hana mutane radawa jarirai sun hada da ‘Arafat’ da kuma ‘Jihad’.
Gwamnati ta kawo wannan doka ne a farkon 2017 kamar yadda rahotonni su ka bayyana domin a dakusar da duk wani kishin addini a kasar Asiyar.
Wannan doka ta na aiki ne a yammacin birnin Xinjiang inda ake da tarin musulmai daga cikin mutanen Uighurs wadanda adadinsu ya haura miliyan 10.
Shekaru uku kenan da gwamnati ta kawo wannan doka, baya ga haka hukumomin kasar Sin ba su daina azabtar da musulman da ke wannan yanki ba.
KU KARANTA: Sheikh Gumi ya bayyana hanyar kawo zaman lafiya a Jihar Kaduna
Gwamnatin Sin ta na zargin musulmai da rike ra’ayin rikau da yunkurin kawo juyin juya-hali. Sai dai jama’a su na ganin tsaurin gwamnati ya jawo hakan.
Jaridar Amurkan da ta fitar da wannan rahoto, ta ce sunayen da aka hana radawa yaran Uighur sun fi 24. Shahararren sunan da ke cikin jerin shi ne ‘Muhammad’.
Muhammad shi ne Annabin karshe a wajen Musulman Duniya don haka ake ji da wannan suna a Musulunci, a yanzu babu sunan da ya kai Muhammad farin-jini.
Sauran sunayen da aka haramta sun hada da “Mujahid” da “Medina.” Mujahid ya na nufin wanda ya amsa kiran Ubangiji, ita kuma Medina ta na nufin birni.
Tun a wancan lokaci jami’an tsaron sun tabbatar da wannan doka. Duk wanda ya saba, zai gamu da barazanar rashin daukar nauyin karatu da lafiyar ‘ya ‘yansa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng