Sunan Muhammad ya zama suna mafi farin jini a kasar Birtaniya
- Sunan Muhammad ya zama suna mafi farin jini a Ingila
- Ya kasance daga cikin sunaye 10 da iyaye ke sanya wa yayansu
- Yanzu haka sunan ya hankada sunan William zuwa gurbi na 10
Hasashe sun nuna cewa sunan Muhammadu ya fice, sannan kuma ya zama mafi farin jinni a kasar Ingila.
A cewar hukumar kididdiga ta kasar Birtaniya ta fitar, bincike ya nuna cewa sunan Muhammad ya samu karbuwa matuka a Ingila.
Ya kuma kasance cikin sunaye 10 da iyaye suka fi sanya wa yaransu kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Sufeto Janar na yan sanda ya ziyarci Umuahia kan ayyukan kungiyar IPOB
Har ila yau Muhammad wanda kafin wannan lokaci ba ya cikin goman farko da suka fi farin jini, a yanzu ya hankada sunan William zuwa gurbi na goma a jerin sunayen da aka fi rada wa yara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng