Warren Buffett: Mai Kuɗi na 7 a Duniya Ya ba da Tallafin Sama da Naira Tiriliyan 1.8

Warren Buffett: Mai Kuɗi na 7 a Duniya Ya ba da Tallafin Sama da Naira Tiriliyan 1.8

  • Mai kudin duniya na bakwai, Warren Buffett ha ya yi gagarumar kyautar kuɗi har dala biliyan 1.1 domin tallafawa al'umma a duniya
  • Hakan na cikin kokarin fitaccen mai kudin wajen ganin ya kyautar da dukkan dukiyar da ya tara a fadin duniya domin tallafawa mutane
  • Tun a shekarar 2006 Warren Buffett ya yi alkawarin sadaukar da dukiyarsa kuma a yanzu haka ya kyautar da kashi 57% na kuɗin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Daya daga cikin masu kudin duniya, Warren Buffett ya cigaba da raba dukiyar da ya tara domin taimakon al'umma.

Warren Buffett ya kuma yi bayanin yadda yake so a raba sauran dukiyarsa idan rai ya yi halinsa.

Buffet
Mai kudi a kudi a duniya ya kyautar da tarin dukiya. Hoto: The Asahi shimbun
Asali: Getty Images

Rahoton India Today ya nuna cewa Buffett ya yi kyautar kudin ne saboda ganin alamar mutuwa za ta iya riskarsa a ko da yaushe.

Kara karanta wannan

An harbe ango a ranar daurin aurensa, amarya ta gigice

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai kuɗin duniya ya yi kyautar $1.1bn

A ranar Litinin babban attajirin na bakwai kuma ɗan shekaru 94, Warren Buffett ya yi kyautar $1.1bn ga cibiyoyin taimakon al'umma.

Buffett ya sanar da rukunin kamfanin Berkshire da ya mallaka a 1965 cewa ya bayar da kyautar makudan kudin.

A yanzu haka dai ana hasashen cewa rukunin kamfanin ya mallaki kadara ta $1.1trn a fadin duniya.

Waɗanda suka samu kyautar Buffett

Rahoton ABC News ya nuna cewa Warren Buffett ya bayar da kyautar makudan kuɗin ne ga cibiyoyin iyalansa da suka haɗa da:

  • Cibiyar Susan Thompson Buffett
  • Cibiyar Sherwood
  • Cibiyar Howard G. Buffet
  • Cibiyar NoVo

Warren Buffett ya tuna da mutuwa

Buffett ya bayyana cewa ya kasance cikin sa'a ganin yadda ya shafe shekaru masu yawa amma duk da haka ya ce ya san lokaci ya kusa.

A shekar 2024 matar Warren Buffett mai suna Susie ta rasu wacce ya ce ya yi tunanin zai rigata mutuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karbo bashin Naira tiriliyan 5.63 daga hannun ƴan kasuwa, ya yi ayyuka 2

A karshe, Warren Buffett ya bukaci ƴaƴansa uku da wani mutum da zai ambata daga baya su jagoranci raba sauran dukiyarsa idan har rai ya yi halinsa.

Raba tallafi: Bankin duniya ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa babban bankin duniya ya ce shirin raba tallafi na musamman na N5000 ga talakawan kasar nan bai yi amfanin komai ba.

Hakan na kunshe cikin rahoton da babban bankin CBN ya fitar mai taken “tasirin raba tallafin kudi ga mata da gidaje a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng