Forbes ta saki jerin masu kudin duniya na 2022: Dangote ne na 130

Forbes ta saki jerin masu kudin duniya na 2022: Dangote ne na 130

  • Mujallar Forbes ta sake jerin masu kudin duniya na shekarar 2022, yan kasar Amurka ne suka mamaye
  • A bisa lissafin mujallar da ta shahara a duniya, akwai bilunoyoyi 2,668 yanzu a fadin duniya
  • Elon Musk ne kan gaba kuma arzikinsa ya ninka na mai kudin Afrika, Dangote, sau goma sha biyar

Mujallar Forbes ta saki jerin sunayen masu kudin duniya inda takwas daga cikin goman farko yan kasar Amurka ne, sannan daya daga Faransa, dayan kuma daga Indiya.

Har ila yau, Amurka ke da masu kudi mafi yawa inda ta tara bulunoyoyi 735.

Independent UK ta ruwaito cewa Elon Musk wanda shine na daya gaba daya kudin bai wuce $2 billion ba a 2012, amma yanzu ya mallaka $218 billion (sama da N90.61trn).

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa su ne a gaba yayin da aka kashe mutane 2, 968 a cikin watanni 3 a 2022

Forbes ta saki jerin masu kudin duniya na 2022: Dangote ne na 130
Forbes ta saki jerin masu kudin duniya na 2022: Dangote ne na 130
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu kudin Afrika

Forbes ta alanta Alhaji Aliko Dangote matsayin mai kudin nahiyar Afrika amma duk da haka bai cikin 100 na farko a duniya.

Dangote ne na 130 da arzikin $14 billion.

Dan Afrikan da ya biyo bayan Dangote shine Johan Ruppert na kasar Afrika ta kudu. Shine na 230 a duniya.

Wani dan kasar Afrika ta kudu, Nicky Oppenheimer, shine na uku a Afrika kuma na 241 a duniya.

Dan kasar Misra ne na hudu a Afrika kuma na 304 a duniya da arzikin $7.7 billion.

Sai dan Najeriya, Mike Adenuga, wanda shine na biyar a Afrika kuma na 324 a duniya.

Attajiran Najeriya na kara kudancewa yayin da sauran na duniya ke ganin ragi

Attajiran Najeriya sun kara matsayi a cikin jerin sunayen masu kudi na duniya na Forbes na baya-bayan nan, wanda ya kunshi arzikin manyan attajirai a duniya, Channels Tv ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ramadan: Wasu muhimman Lokuta 5 masu Albarka da ya kamata Musulmi ya Amfana da su

Habakar tasu ta zo ne duk da hauhawar farashin kayayyaki a duniya wanda ya haifar da girgizar tattalin arziki bayan barkewar cutar ta Korona da kuma yakin Rasha da Ukraine.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya samu karuwar arzikinsa daga dala biliyan 11.5 a 2021 zuwa dala biliyan 14 a 2022.

Mike Adenuga, attajiri na biyu a Najeriya, ya karu daga dala biliyan 6.1 zuwa dala biliyan 7.3.

Abdulsamad Rabiu, dan Najeriya na uku a jerin sunayen masu kudin kasar nan, ya ga kari a arzikinsa daga dala biliyan 4.9 zuwa dala biliyan 6.9.

Asali: Legit.ng

Online view pixel