"An Rataya Mana Jakar Tsaba:" IMF Ya Fadi Abin da Ya Sani kan Cire Tallafin Fetur

"An Rataya Mana Jakar Tsaba:" IMF Ya Fadi Abin da Ya Sani kan Cire Tallafin Fetur

  • Asusun bayar da lamuni na duniya ya barranta kansa da cire tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi karkashin Tinubu
  • Daraktan Asusun na nahiyar Afrika, Mista Abebe Selassie ne ya bayyana haka a Washington DC a taron IMF da bankin duniya
  • Sai dai Mista Selassie ya yaba da cire tallafin, amma ya bukaci gwamnatin ta samar da hanyar rage wahalar da talakawa ke sha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Washington DC - Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya wanke kansa daga zargin cewa shi ne kanwa uwar gami wajen cire tallafin fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Haka ya shiga ofis babu manufa:" Obasanjo ya zargi gwamnatin Tinubu da aiki da ka

Wannan na zuwa bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur tun ranar da ya sha rantsuwar aiki.

Tinubu '
IMF ta wanke kanta daga zargin tunzura cire tallafin fetur a kasar nan Hoto: @RahmaneSARR/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Daraktan nahiyar Afrika na Asusun IMF, Abebe Selassie ya kare IMF daga zargin tunzura Najeriya ta yi karin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IMF ta barranta kanta da cire tallafin fetur

Daraktan nahiyar Afrika na Asusun lamuni na duniya (IMF), Abebe Selassie ya ce ba shi da wani shiri da ke gudana a halin yanzu a Najeriya.

Mista Abebe Selassie ya ce tsakaninsa da Najeriya shawara ce kawai, amma ba shi da hannu a umarnin da Bola Tinubu ya bayar kan cire tallafin man fetur.

Menene ra'ayin IMF kan tsarin Najeriya?

Asusun IMF ya bayyana cewa tsarin da gwamnatin Najeriya ke amfani da shi zai cicciba tattalin arzikin Najeriya a shekaru da yawa masu zuwa.

Kara karanta wannan

Raba kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai ya hango makomar Najeriya

Mista Abebe Selassie ya ce amma akwai bukatar gwamnatin kasar ta gaggauta samar da hanyoyin saukakawa talakawa halin da matakan su ka jefa su.

IMF ya ce kudin Najeriya na farfadowa

A wani labarin kun ji cewa Asusun bayar da lamuni na duniya ya ce alamu sun nuna yadda kudin Najeriya,wato Naira ya fara farfadowa a kasuwar duniya.

Asusun ya fadi haka ne yayin da darajar Naira ya haura N1600 a kasuwar musayar kudade, kuma ta ce ana samun cigaba saboda matakan da CBN Ke dauka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.