Shahararren Jarumin Fim Zai Bude Makarantar Koyon Kwallon Kafa a Jihar Arewa
- Wani shahararren jarumin fina finai, Pascal Atuma ya shirya bude makarantar horar da 'yan wasan kwallon kafa a Katsina
- Pascal Atuma ya bayyana hakan ne a taron kulla yarjejeniya tsakanin kungiyarsa, gwamnatin Katsina da makarantar Bondy
- A taron kulla yarjejeniyar a Faransa, jarumin ya ce zai tabbatar an tsakulo hazikan matasa a Katsina domin ba su hoto a wasanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Faransa - Fitaccen jarumi kuma mai shirya fina-finai, Pascal Atuma, ya bayyana hadin gwiwarsa da gwamnatin jihar Katsina domin "koyar da hazikan matasa a Najeriya".
Pascal Atuma ya ce kwarewarsa a harkar fim, wakoki da kwallon kafa, ya ba shi fikirar gane muhimmancin horar da matasa a wasanni har su zama wani abu.
Bayanin jarumin fim din na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya aikawa jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumi zai horar da 'yan kwallo a Katsina
Jarumi Pascal Atuma ya bayyana cewa:
“Wasu al’ummomi sun samu ci gaba sosai wajen bunkasa hazakar matasansu, kuma dole ne Nijeriya ta ba da fifiko wajen karfafa matasa masu wannan hazakar.
"Wannan ne ya sa na yanke shawarar haɗin gwiwa tsakanin Tabic sporting outfit, ma'aikatar matasa da wasanni ta jihar Katsina/KFA da makarantar Bondy a Faransa."
Ya kara da cewa wannan hadakar za ta taimakawa wajen samar da hazikan matasa a kwallon kafa daga Katsina, tare da ba su horo har sai sun iya gogayya da 'yan wasan duniya.
Jarumi ya kulla yarjejeniya da Katsina
Premium Times ta rahoto Atuma ya kara da cewa, an kammala cimma yarjejeniya tare da rattaba hannu a taron karshe da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa.
A wajen taron, gwamnatin jihar Katsina ta samu wakilcin kwamishinan matasa da bunkasa wasanni, Lawal Zakari da shugaban makarantar KFA, Ahmed Mohammed.
Sauran wakilan jihar sun hada da shugaban kwamitin wasanni na majalisar dokokin Katsina, Hon. Sani Bello.
Ya kara da cewa, makarantar Bondy ta samu wakilcin babban jami’in gudanarwa, Aacim Zahiri; daraktan wasanni, Jamel Zahiri yayin da shi ya wakilci kungiyar Tabic FC.
An yi hargitsi a wasan Katsina da Kwara
A wani labarin, mun ruwaito cewa an tashi baran-baran a wasan gasar cin kofin Firimiyar Najeriya da aka buga tsakanin Katsina United ta takwarar ta Kwara United.
Rai ya baci bayan alkalin wasa ya hana Katsina bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan dan wasan baya na Kwara ya saka hannu ya hana kwallo shiga zare.
Asali: Legit.ng