An tashi baran-baran tsakanin Katsina United da Kwara United a gasar Firemiya ta kasa
- Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United da takwarar ta Kwara United sun tashi baran-baran bayan Katsina ta sha kashi a gidan Kwara United
- Bayan tashi daga wasa, mai kociyan kungiyar Kwara ya zagi kociyan kungiyar Katsina United
- An bayyana abinda alkalin wasa, Sam Agba, ya yi a matsayin abin kunya
An tashi baran-baran a wasan gasar cin kofin Firemiya na kasa da aka buga tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ta takwarar ta Kwara United a karshen satin da ya wuce.
Rai ya baci bayan alkalin wasa, Sam Agba, dan asalin jihar Kuros Riba ya hana kungiyar Katsina bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan dan wasan baya na kungiyar Kwara United, Chinedu Sunday, ya saka hannu ya hana kwallon da dan wasan Katsina United, Ajah Joseph, ya buga shiga zare.
Lamarin ya fusata mahukunta da 'yan wasan kungiyar Katsina United kafin daga bisani bayan tashi daga wasa kociyan kungiyar Kwara United ya takali kociyan kungiyar Katsina United har ta kai ga an kusa bawa hammata iska.
Masu nazarin wasan kwallon kafa sun bayyana abinda alkalin wasa, Agba, ya yi a matsayin abin kunya.
DUBA WANNAN: Gaba kura baya hayaki: Matan da aka kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram na cikin halin tsaka wuya
Alkalin wasan ya hana kungiyar Katsina United wani bugun daga kai sai mai tsaron bayan da an kayar da dan wasa Destiny Ashadi a cikin akwatun ragar gidan kungiyar Kwara United.
An dade ana kokawa a kan halayyar alkalan wasan gasar Firemiya ta kasa bisa yadda suke danne kungiyar baki da gan-gan.
An zura wa kungiyar Katsina United kwallo biyu a raga yayin da suka yi nasarar zura kwallo daya a ragar Kwara United.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng