Fasinjoji Sun Kidime, Matukin Jirgin Sama Ya Mutu yayin da Ake Gudu a Samaniya

Fasinjoji Sun Kidime, Matukin Jirgin Sama Ya Mutu yayin da Ake Gudu a Samaniya

  • Wani jirgin saman Turkiyya ya yi saukar gaggawa a filin jirgin JFK da ke birnin New York da matukin jirgin ya mutu ana tsakiyar tafiya
  • Jirgin ya taso ne daga Seattle a ranar Talata da zummar sauka a Istanbul lokacin da abin ya faru, kamar yadda kamfanin ya fitar da sanarwa
  • Mai magana da yawun kamfanin jiragen, Yahya Üstün ya yi karin haske kan matakin da aka dauka na kai fasinjoji zuwa Instanbul

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Turkiyya - A ranar Laraba ne wani matukin jirgin saman Turkiyya ya mutu yayin da jirgin ke kan hanyarsa daga Seattle zuwa Istanbul.

Kyaftin din jirgin wanda aka bayyana a matsayin Ilcehin Pehlivan mai shekaru 59, ya suma ne bayan da jirgin kirar Airbus 350 ya tashi daga Seattle.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya bayyana abin da zai kawo zaman lafiya

Matukin jirgin sama ya mutu yana tsaka da tuki
Matukin jirgin saman Turkiyya ya mutu yana tsaka da tuka jirgi zuwa Instanbul. Hoto: GordZam, Chris Sattlberger
Asali: Getty Images

Matukin jirgi ya mutu a samaniya

Bayan duk wani kokari na farfado da shi ya ci tura, ma'aikatan jirgin sun yanke shawarar yin saukar gaggawa a New York, a cewar rahoton Bloomberg.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da kamfanin jiragen saman Turkiyyar ya fitar an ce tun kafin jirgin ya sauka kasa, direban ya ce 'ga garinku nan'.

An ce Kyaftin Pehlivan ya fara aiki ne da kamfanin jirgin saman Turkiyya tun a shekarar 2007.

Wani hali fasinjojin jirgi ke ciki?

Kamfanin jiragen ya ce an yi wa matukin jirgin gwajin lafiya na karshe a cikin watan Maris, kuma ba a samu wata matsala da za ta hana shi gudanar da aikinsa ba.

Mai magana da yawun kamfanin jiragen saman Turkiyya, Yahya Üstün ya fitar da sanarwa a shafinsa na X bayan faruwar lamarin yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya bayyana dalilin barkewar rikici a jihar Rivers

"Matukin jirgin mu na Airbus 350, jirgin TK204 daga Seattle zuwa Istanbul ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tuki."

Sanarwar ta ce za a kwashi fasinjojin TK204 da aka yi saukar gaggawa da su a New York zuwa Instanbul daga filin jirgin kasa da kasa na JFK.

Matukin jirgin sama ya mutu a bandaki

A wani labarin, mun taba ruwaito cewa matukinwani jirgin sama da ya taso daga Miami zuwa Chile, ya mutu a cikin bandaki yayin da jirgin ke tsula gudu a sararin samaniya.

An ce matukin wanda aka bayyana sunansa da Ivan Andaur, ya fara jin alamar rashin lafiya bayan sa'o'i uku da tashin jirgin na kamfanin LATAM daga Florida zuwa Santiago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.