Abun bakin ciki! Ga hotunan matukin jirgin da ya mutu a hatsarin jirgin sojin sama

Abun bakin ciki! Ga hotunan matukin jirgin da ya mutu a hatsarin jirgin sojin sama

- Wani jirgi mallakar rundunar sojin sama yayi hatsari a Kaduna

- Wani matukin jirgi dake kan aiki ya rasa ransa a hatsarin

A baya Legit.ng ta rahoto labarin mutuwar Kyaftin Adamu Gabriel Ochai, kwararen matukin jirgin rundunar soji wanda ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama. An rahoto cewa matukin ya kasance shi kadai a kan aiki lokacin da hatsarin ya afku.

Hatsarin jirgin ya faru da misalin karfe 4:25 na ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta a makarantar soji NDA dake hanyar filin jirgin sama na Kaduna.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Olatokunbo Adesanya, yace wani matukin jirgi daya ya rasa ransa a hatsarin.

Abun bakin ciki! Ga hotunan matukin jirgin da ya mutu a hatsarin jirgin sojin sama
Marigayin da matarsa

Adesanya ya bayyana cewa shugaban hafsan sojin sama ya umurci sashin bincike da su gano musabbabin afkuwar hatsarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: shugaba Buhari na ganawa da shugabannin APC da PDP (bidiyo)

Abun bakin ciki! Ga hotunan matukin jirgin da ya mutu a hatsarin jirgin sojin sama
Marigayin da iyalan sa

Wani makusancin marigayin ya buga hotunansa a shafin Faceboo, inda yake alhinin mutuwar dan uwan nasa.

Marigayin ya mutu ya bar matar aure da yara mata guda uku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng