Attajirin Duniya Elon Musk ya Shiga Matsala, Brazil ta Hana Amfani da Manhajar X
- Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin kasar Brazil ta toshe hanyoyin shiga manhajar X a kasarta mai dauke da mutane kimanin 200m
- An ce haramta amfani da manhajar X ya samo asali ne daga ja-in-jar da aka samu tsakanin Elon Musk da alkalin kotun Kolin Brazil
- Kotun Kolin Brazil ta umarci Elon Musk ya sauke wasu asusun 'yan kasarta daga X, amma attajirin ya ce hakan ya saba dokar 'yanci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Brazil - A ranar Asabar, 31 ga watan Agusta Kotun Kolin Brazil ta haramta tare da toshe amfani da X (Twitter) a kasar mai dauke da mutane kimanin miliyan 200.
An ce Alexandre de Moraes, alkalin Kotun Kolin ya toshe X bayan shugaban kamfanin, Elon Musk ya ki ya martaba umarnin kotun na sauke wasu asusu da ke kan manhar.
An toshe manhajar X a Brazil
Jaridar New York Times ta ruwaito cewa wannan dakatarwar ya jawo babban cikas ga kokarin attajirin duniyar na mayar da X wani dandali na fadin ra'ayin jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alexandre de Moraes, ya umarci hukumar sadarwar Brazil da ta toshe hanyar shiga X a cikin kasar saboda kamfanin ba shi da ofishi a Brazil.
Elon Musk ya rufe ofishin X na Brazil a makon da ya gabata bayan Mai shari'a Moraes ya yi barazanar kama shi saboda yin watsi da umarninsa na sauke wasu asusun X.
Rigimar Musk da alkalin Brazil
Mahajar X ta ce ta na kallon umarnin da Mai shari'a Moraes ya bayar na rufe wasu asusun X saboda saba ka'idojin Brazil a matsayin karya doka kuma zai wallafa batun ga duniya.
"Fadin albarkacin baki shi ne tubali ne na dimokuradiyya kuma wani alkali da ba a zaba ba a Brazil yana kokarin rusa shi saboda wasu dalilai na siyasa."
- A cewar Elon Musk, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a ranar Juma'a.
Za a fara biyan kudi a X
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kamfanin Twitter da ta sauya suna zuwa X, Elon Musk ya bayyana cewa manhajar X za ta fara cajar kudi daga masu amfani da mzanhajar.
Elon Musk ya bayyana cewa wannan na daga cikin matakin da kamfanin ke shirin dauka domin magance matsalar masu amfani da mahajar X suna yada labaran karya.
Asali: Legit.ng