FG Za Ta Sake Haramta Twitter? Lai Mohammed Ya Bayyana Abubuwa Masu Muhimmanci

FG Za Ta Sake Haramta Twitter? Lai Mohammed Ya Bayyana Abubuwa Masu Muhimmanci

  • Ministan watsa labarai, Lai Mohammed, ya yi magana kan siyan Twitter da aka yi a baya-bayan nan da shirin gwamnatin tarayya
  • A wurin taron ma'aikatun gwamnati a Abuja a ranar Alhamis, Mohammed ya ce rahoton da ke cewa FG na son rufe Twitter ba gaskiya bane
  • Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da niyyar hana yan kasar amfani da Twitter ko wata dandalin sada zumunta, amma suna sa ido a yayin da Elon Musk ya siya kamfanin

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya (FG) ta ce tana sa ido sosai kan dandalin sada zumunta na Twitter, bayan samun canjin mammalakin kamfanin, Daily Trust ta rahoto.

Tunda farko, attajirin kasar Amurka, Elon Musk, ya siya Twitter kuma yana ta yin manyan canje-canje.

Lai da Twitter
Shin FG Za Ta Sake Rufe Twitter" Lai Mohammed Ya Yi Maganganu Masu Muhimmanci. Hoto: Photo credit: Federal Ministry of Information and Culture, Nigeria, theverge.com
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FG ta yi karin haske game da Twitter a Najeriya

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, a wurin taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba, ya yi magana game da shirin da gwamnatin tarayya ke yi kan batun, The Punch ta rahoto.

Lai Mohammed ya ce duk da cewa gwamnati bata da niyyar rufe kafafen sada zumunta kuma, ta yanke shawarar cewa ba za ta kyalle duk wani kafar sada zumunta da ke yada labaran karya da kalaman batanci ko kiyayya ba.

A cewar Mohammed, gwamnati ta cigaba da tuntubar kamfanonin sada zumunta daban-daban irinsu Facebook (Meta), Google (masu YouTube) da Twitter, rahoton Vanguard.

Kalamansa:

"Bari in fada wannan: Muna sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Twitter. Ba niyyar mu bane rufe kowanne dandalin sada zumunta ko dakile damar tofa albarkacin baki. Ba haka bane. Abin da ya faru da Twitter sanannen lamari ne ga kowa."

Elon Musk Ya Kori Shugaban Tuwita Da Wasu Manyan Shugabanni 2 - Awanni Bayan Ya Siya Kamfanin

A wani rahoton, Elon Musk, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin Tesla Inc., ya sallami manyan shugabannin kamfanin Tuwita, The Cable ta rahoto.

Hakan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan ya kammala cinikin siyan Tuwita, kuma bayan Musk ya yi alkawarin ba zai kori ma'aikata ba.

Wadanda aka sallama sun hada da; Parag Agrawal, shugaban Tuwita, Ned Segal, babban jami'in kudi; da Vijaya Gadde, babban lauyan kamfanin kuma shugaban tsare-tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel