'Yan Bindiga Sun Fara Baje Kolin Ayyukansu a TikTok, an Hango Illar Hakan Ga Tsaro

'Yan Bindiga Sun Fara Baje Kolin Ayyukansu a TikTok, an Hango Illar Hakan Ga Tsaro

  • Kasashe da dama sun haramta amfani da dandalin TikTok yayin da wasu kuma suka sanya takunkumi ga wadanda za su yi amfani da shi
  • A Najeriya, an samu bayyanar 'yan bindiga a TikTok, inda suke tallata kuɗaɗen da suka karɓa na fansa kuma suna yin bidiyon ne cikin izza
  • Tsohon ministan sadarwa da tattali na zamani, Isa Ibrahim Pantami ya ce ma damar ana son magance matsalar tsaro, a yi amfani da NIN

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A fadin duniyar nan, akwai kasashen da ke ci gaba don taƙaitawa ko hana amfani da dandalin TikTok saboda tsaron ƙasa, tsaron bayanan jama'a da damuwar canjawar ɗabi'ar mutane.

Matakan da kasashen duniyar ke dauka kan dandalin ba zai rasa nasaba da barazanarsa ga tsaron ƙasa, satar bayanan jama'a da kuma canja ɗabi'un mutane ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji miyagun 'yan ta'adda a jihar Kaduna

Yadda 'yan bindiga suka fara mamaye TikTok da matakan da kasashe suka dauka
Kasashen duniya sun dauki mataki kan TikTok yayin da 'yan bindiga suka fara amfani da dandalin. Hoto: @drpenking/X, Dan Kitwood/Getty
Asali: Twitter

'Yan bindiga na shiga TikTok

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa wadannan dalilansun kara nuna bukatar kare kasashe daga barazanar da ake samu daga dandalin TikTok mallakar dan kasar Sin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Najeriya, ana fargabar bayyanar 'yan bindiga a dandalin TikTok. A mafi yawan lokuta suna tallata kuɗaɗen da suka karɓa daga waɗanda aka yi garkuwa da su cikin izza.

Kasashe da yawa ko dai sun dakatar da TikTok gaba daya ko sun kakaba masa takunkumi saboda fargabar wata kasa na iya satar bayanan jama'a ta hanyar da zai cutar da su.

Kasashen da suka haramta TikTok

  1. Senegal
  2. Somalia
  3. Korea ta Arewa
  4. Afghanistan
  5. Indiya
  6. Iran
  7. Uzbekistan
  8. Kyrgyzstan

Bidiyon 'yan bindiga a TikTok

Zanagazola Makama ya ce amfani da TikTok da kungiyar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda ke yi zai haifar da babbar matsala domin dandalin na sada su ga dimbin jama’a a duniya.

Kara karanta wannan

Digiri dan Kwatano: Gwamnati ta lissafa jami'o'in Benin, Togo da ta amince da su

Ya ce bayanan da suke dorawa a TikTok an tsara su ne domin jan hankalin mutane su bi akidarsu, wanda zai sauƙaƙa wa waɗannan ƙungiyoyi wajen samun sababbin mabiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Illolin TikTok ga tsaron kasa

Zagazola Makama ya ce TikTok na ci gaba da zama wani dandali mai karfi da kungiyoyin ta'addanci ke amfani da shi wajen neman sababbin mabiya masu irin akidarsu.

Ya ce babban misalin shi ne bayyana 'yan Boko Haram a TikTok, wadanda ke tattaunawa kai tsaye da mabiyansu da kuma tallata mummunar akidarsu.

Mai sharhi kan lamuran tsaron ya ce barin TikTok sakaka yana bude kofa ga 'yan ta'adda su rika ribatar mutane masu raunin imani, wanda ke kai ga karuwar ta'addanci.

"Ayi amfani da NIN" - Pantami

Tsohon ministan Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya jaddada cewa ma damar gwamnati za ta yi amfani da fasar bin diddigin NIN to za a magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

DHQ: Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda sama da 150, sun kama wasu 302 a Najeriya

Isa Pantami wanda ya rike minista tattali na zamani a mulkin Muhammadu Buhari, ya ce ta hanyar NIN da rijistar layukan waya, za a gano duk inda 'yan bindiga suke.

A cewar Pantami:

"In dai za a yi aiki da bayanan da muka tattara na miliyoyin 'yan kasar daga NIN da rijistar layukan waya, babu wanda zai yi barna da ba za a gano shi ba."

Duba bidiyon malamin a kasa:

TikTok: Dan bindiga ya saki bidiyo

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani dan bindiga ya wallafa sabon bidiyo a dandalin TikTok inda ya ke nuna kudin fansar da ya karba da kuma bindigarsa.

Wannan lamari ya harzuka wasu 'yan Najeriya da suke ganin jami'an tsaro sun gaza kama 'yan bindigar duk da cewa yanzu sun fara amfani da TikTok.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.