Yadda Matatar Dangote Za Ta Kawo Cikas ga Harkar Mai a Turai, OPEC Ta yi Karin Haske

Yadda Matatar Dangote Za Ta Kawo Cikas ga Harkar Mai a Turai, OPEC Ta yi Karin Haske

  • Rahoton OPEC ya nuna cewa matatar man Dangote na shirin zama kadangaren bakin tulu ga masana'antar man Turai musamman ta NWE
  • Rahoton ya bayyana irin tasirin da matatar Dangote ke da shi a idon duniya, musamman idan ta kulla kawance da Gabas ta Tsakiya da Mexico
  • An ce Turai ce babbar mai sayen tataccen mai kuma ta dogara ne kan shigo da mai daga Asiya da Amurka lamarin da zai budewa Dangote hanya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rahoto ya nuna cewa babbar matatar man duniya da aka gina a Najeriya mallakin attajiri Aliko Dangote za ta kawo cikas ga harkar mai a Turai.

An ce matatar man Dangote za ta zama tamkar kadangaren bakin tulu ga Turai musamman ma masana'antar mai da gas a Arewa maso Yammacin Turai (NWE).

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

OPEC ta yi magana kan tasirin matatar Dangote a kasuwar man Turai
OPEC ta ce matatar Dangote za ta kawo cikas ga kasuwar man Turai. Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin rahoton da OPEC ke fitarwa na wata wata wanda ta saki a Nuwamban 2024, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote za ta girgiza duniyar mai

Rahoton OPEC ya lissafa matatar Dangote a cikin manyan masu samar da dizal da man jiragen sama wadda za ta zamo barazana ga masana'antar mai da gas ta Turai.

Sai dai rahoton ya ce matatar man Dangote idan har ta kai ga gaci, to ba shakka za ta zamo abar kwatance a duniya kuma za ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya.,

Idan ba a manta ba, wani kamfanin kasuwanci da bin diddigin jiragen ruwa (S&P) ya ce matatar Dangote ta dala biliyan 20 za ta girgiza kasuwar mai ta duniya.

Matatar Dangote za ta kawo cikas ga Turai

Jaridar The Sun ta ce rahoton OPEC ya fayyace irin cikas da Turai za ta samu idan matatar Dangote ta fara karba da raba mai a Gabas ta Tsakiya da kuma matatar Olmeca ta Mexico.

Kara karanta wannan

Jama'a sun dimauce bayan wuta ta tashi a gidan mai bayan zanga-zanga ta lafa

OPEC ta bayyana cewa:

"Turai ce babbar mai sayen tataccen mai kuma ta dogara ne kan shigo da mai daga Asiya da Amurka bayan da Tarayyar Turai ta haramta amfani da dizal na Rasha a Turai."

Sai dai, matatar man Dangote, na shirin fara mu'amala da kasuwannin Turai da dama bayan da kamfanonin mai na duniya suka daina samar da danyen manta.

Dangote zai sayar da hannun jarin matata

A wani labarin, mun ruwaito cewa attajiri na biyu mafi kudi a Afrika, Aliko Dangote na shirin sayar da kaso 12.72 na hannun jarin matatar mansa bayan NNPC ta hakura da saye.

An ce idan Dangote ya sayar da hannun jarin, to akwai yiwuwar zai biya wani babban bashi da kudin ne, wanda wa'adin bashin ke karewa a karshen watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.