Matatar Mai ta Dangote zata kashe kasuwar matatun Turai da muke sayen mai

Matatar Mai ta Dangote zata kashe kasuwar matatun Turai da muke sayen mai

- Matatar man fetur ta Dangote barazana ce ga turai

- Dama Najeriya ta dogara da shigo da man fetur daga turai

- Matatar tana daya daga cikin manyan matatun man fetur a duniya

Matatar Mai ta Dangote zata kashe kasuwar matatun Turai da muke sayen mai
Matatar Mai ta Dangote zata kashe kasuwar matatun Turai da muke sayen mai

Matatar man fetur ta Dangote da ake ginawa a Legas babbar barazana ce ga turai, inda Najeriya ta dogara wajen shigo da man fetur.

Daraktan yada labarai na harkokin kasuwancin man S&P Global Platts, Andrew Bennington, ya sanar da hakan a taron kungiyar na ranar Alhamis cewa fara aikin matatar man fetur din zai iya kawo sanadin rufe wasu daga cikin matatun man fetur na turai.

Yace "A Afirka, matatar man fetur din Dangote babban labari ne, daya daga cikin manyan matatun man fetur na duniya aka gina a Najeriya, wanda da alamar zai samar da dukkan man fetur din da Najeriya take bukata".

Wannan kiri kiri ya kasance barazana ga matatun man fetur din turai saboda Najeriya a gurin su take samun man fetur.

DUBA WANNAN: 'Akpabio ne zai zama shugaban majalisar dattijai'

"Zan iya cewa nasan makomar matatun man fetur din turai, wanda ba makoma bace mai kyau"

Kamar yanda Bonnington ya fada, turai itace ja gaba gurin samar da kayayyakin man fetur ga Najeriya, da kusan kashi 75 cikin dari na fetur din da ake amfani dashi a kasar ana shigo dashi ne daga Nahiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng