Matatar Man Fetur ta Dangote na Barazanar janyo rufe wasu Kamfanoni a 'Kasashen Turai

Matatar Man Fetur ta Dangote na Barazanar janyo rufe wasu Kamfanoni a 'Kasashen Turai

Za ku ji cewa katafaren kamfanin matatar man fetur da fittacen Attijirin nan, Alhaji Aliko Dangote ke ginawa a jihar Legas, zai kasance barazana ga wasu matatun man fetur dake kasashen Turai wadanda Najeriya ta dade da dogaro da su wajen shigo da man fetur cikin kasar nan.

Kamar yadda wani Babban Darakta na ma'aikatar makamashi, Andrew Bonnington a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana, akwai yiwuwar da zarar matatar man fetur ta Dangote ta fara aiki gada-gadan za ta yi sanadiyar rufe wasu matatun ma fetur dake kasashen nahiyyar Turai.

A yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch, Andrew ya bayyana cewa, matatar man fetur ta Dangote da ake ginawa a kasar nan ta Najeriya ta na daya daga cikin manya-manya a fadin duniya.

Matatar Man Fetur ta Dangote na Barazanar janyo rufe wasu Kamfanoni a 'Kasashen Turai
Matatar Man Fetur ta Dangote na Barazanar janyo rufe wasu Kamfanoni a 'Kasashen Turai

Yake cewa, da zarar an kammala ta akwai yiwuwar ta biya kaso mafi tsoka ko kuma dukkanin bukatuwar man fetur ta kasar nan da hakan zai kasance kalubale gami da barazana ga matatun man fetur dake nahiyyar turai sakamakon tunkudo ma fetur da suke yi cikin kasar nan.

Ya ci gaba da cewa, ba zai iya bayyana tabbatace nakasun da wannan katafaren kamfani zai janyowa kasashen na Turai ba, sai dai ko shakka babu za su tagayyara kwarai da aniyya sakamakon dogaro da Najeriya ta dade da yi a kansu.

KARANTA KUMA: Rayuka 21 sun salwanta yayin da wani Jirgin Ruwa ya dilmiya a jihar Sakkwato

A cewar sa, nahiyyar Turai ita ce kan gaba wajen shigo da man fetur da ma'adanan sa cikin Najeriya, inda ake shigo da kaso 75 cikin 100 na man fetur da kasar nan ke amfana daga nahiyyar.

A makon da ya gabata ne tataccen attajirin ya bayyana cewa, ana sa ran wannan katafaren kamfani zai fara aiki gadan-gadan a shekarar 2020.

Dangote wanda ya kasance mutum mafi tarin arziki a nahiyyar Afirka, yana gina katafaren kamfanin matatar man fetur mai ikon samar da ganguna 650, 000 a kowace rana domin tallafawa Najeriya wajen rage dogaro akan shigo da man fetur da ma'adanan sa cikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng