Gwamnatin Tinubu Ta Gargadi Yan Najeriya Bayan Zanga Zanga Ta Barke a Birtaniya

Gwamnatin Tinubu Ta Gargadi Yan Najeriya Bayan Zanga Zanga Ta Barke a Birtaniya

  • Gwamnatin tarayya ta tura gargadi gan yan Najeriya yayin da aka samu wata zanga zanga ta barke a kasar Birtaniya
  • Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ce ta fitar da sanarwar a yau Alhamis yayin da zanga zangar ke cigaba a kasar
  • Mutanen Birtaniya sun fara zanga zanga ne a makon da ya wuce inda lamarin ya rikice ya koma sace sace da kone kone

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Gwamnatin Najeriya ta gargadi yan Najeriya musamman mazauna kasar Birtaniya kan zanga zanga da ta barke a kasar.

Rahotanni na nuna cewa an samu kashe kashe da kone kone yayin da zanga zanga ke kara daukar salo a Birtaniya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Birtaniya
Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya kan zanga zanga a Birtaniya. Hoto: SOPA Images
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gargaɗin ya fito ne daga ofishin harkokin wajen Najeriya a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene dalilin zanga zanga a Birtaniya?

Mutanen kasar Birtaniya suna zanga zanga ne tare da rera wakokin kin baki 'yan gudun hijira zuwa kasarsu.

Rahotanni da suka fito daga baya baya sun nuna cewa lamarin ya jawo mutuwar yan mata uku da lalata dukiya mai yawa.

Birtaniya: Gargaɗin da Najeriya ta yi

The Guardian ta wallafa cewa ofishin harkokin wajen ya bukaci yan Najeriya da da suke Birtaniya ko suke shirin tafiya da su yi taka-tsantsan.

An bukaci yan Najeriya da su kaucewa shiga zanga zanga ko taron jama'a da duk wani taron siyasa a kasar Birtaniya domin kaucewa barazana.

Karin matakin kariya ga yan Najeriya

Haka zalika ofishin harkokin wajen ya bukaci yan Najeriya su kasance suna kai hankali kan dukkan abubuwan da suke faruwa a kasar Britaniya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun nuna turjiya bayan an yi musu ruwan borkonon tsohuwa

Bayan haka ofishin ya tanadar da imel da lambar waya da za a rika kira da zarar dan Najeriya ya shiga matsala a kasar. Ga imel da lambar wayar:

Imel: hc@nigeriahc.org.uk

Lambar waya: +442078391244

Yan sanda sun magantu kan kashe matasa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kano ta yi bayani kan mutanen da ake zargi ta harbe a yayin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kakakin yan sanda a jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana halin da ake ciki da fadin asalin abin da ya jawo lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng