Zanga Zanga: Bayan Shan Suka, Yan Sanda Sun Yi Bayani Kan Kashe Mutane a Kano

Zanga Zanga: Bayan Shan Suka, Yan Sanda Sun Yi Bayani Kan Kashe Mutane a Kano

  • Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kano ta yi bayani kan mutanen da ake zargi ta harbe a yayin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Kakakin yan sanda a jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana halin da ake ciki da fadin asalin abin da ya jawo lamarin
  • Yan sanda sun yi bayani ne bayan al'ummar jihar Kano da Najeriya sun yi korafi kan zargin kisan da suka yiwa fararen hula a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar yan sanda a jihar Kano ta yi bayani kan mutanen da ake zargi jami'anta sun kashe yayin zanga zanga.

Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana halin da ake ciki kan lamarin.

Kara karanta wannan

Zargin kashe masu zanga zanga: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin bincikar jami'an tsaro

Yan sanda
Yan sanda sun yi magana kan kashe mutane a Kano. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Haruna Abdullahi Kiyawa ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sandan Kano sun ce matasa sun karya doka

Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an samu wasu matasa da suka fito zanga zanga bayan an saka dokar taƙaita zirga zirga a jihar.

A cewar yan sanda, bayan fitowarsu daga unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo sai suka fara yunkurin yin satar kayan mutane amma yan sanda suka yi korin hana su.

Matasa sun nemi kai hari ga yan sanda

Abdullahi Kiyawa ya ce bayan yan sanda sun hana matasan sata sai suka yi yunkurin kai musu hari.

Amma yan sanda suka nemi taimakon karin jami'an tsaro suka kare kansu kamar yadda doka ta tanadar.

Yan sanda sun kashe mutane Kano?

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka hallaka Bayin Allah lokacin zanga zanga a jihar Kano

Kiyawa ya bayyana cewa bayan yan sanda sun kare kansu ne sai suka samu labarin cewa an harbi wasu mutane yayin da abin ya faru.

Saboda haka ya ce kwamishinan yan sanda ya bayar da umurnin yin bincike kan yadda za a gano gaskiyar lamarin tare da ɗaukar mataki.

Zanga zanga: PDP ya shawarci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa jami'yyar adawa ta PDP ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan zanga zanga.

PDP ta ambaci abubuwan da ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi domin kwantar da hankalin matasan Najeriya cikin sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng